Naira ba ta ji da dadi ba a karshen makon jiya

Naira ba ta ji da dadi ba a karshen makon jiya

- Dala ta ba Naira kashi a karshen wancan makon

- Duk da irin kokarin da CBN ke yi abin ya faskara

- Da farkon makon dai Naira ta babbako a kasuwar canji

Za ku ji cewa duk da irin kokarin da Babban bankin kasar na CBN ke yi Naira ta sha kasa a karshen wancan makon da ya wuce.

Naira ba ta ji da dadi ba a karshen makon jiya

Hoton kudin Naira da Dala hannun 'yan canji

Mun samu labari cewa Darajar Naira yayi kasa da N1 tak a zuwa Ranar Juma'a wanda dai ana sa rai zuwa wannan makon nan abin ya kara sauki. Dalar ta koma N366 a kan N365 da ta ke a baya kadan.

KU KARANTA: Buhari ya rusa tattalin arzikin Najeriya-PDP

Naira ba ta ji da dadi ba a karshen makon jiya

Gwamnan Babban bankin kasar nan CBN

Pounds Sterling ta Ingila kuma na nan a kan N468 yayin da Euro na kasar Turai ke wajen N412. Sai dai a wajen 'yan canji na BDC abin bai kai haka ba. A kan samu Dalar ne a kan N363 a karshen makon jiya.

A banki dai ana saida Dalar Amurka a kan N306. Pounds Sterling da EURO kuma su kan tashi a man N395 da N348. Sai dai yanzu neman Dalar zai karu saboda an amince da kasafin kudin bana.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko 'Yan Najerya sun gaji da Shugaba Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel