Babban dalilin da ya sa Sanatoci ke kokarin tsige Osinbajo

Babban dalilin da ya sa Sanatoci ke kokarin tsige Osinbajo

- 'Yan Majalisa na yunkurin tsige Mukaddashin Shugaban Kasa Osinbajo

- Sanatocin sun fake ne da maganar Shugaban EFCC Ibrahim Magu

- Sai dai wani bincike daga Jaridar Daily Trust ya nuna ashe ba a nan ta ke ba

Sanatoci sun hurowa Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo wuta ya janye kalaman sa game da Shugaban EFCC Ibrahim Magu ko ya bar kujerar sa.

Babban dalilin da ya sa Sanatoci ke kokarin tsige Osinbajo

Shugaban Sanatoci tare da Yemi Osinbajo

1. Karar Bukola Saraki

Osibanjo yace Majalisa ba ta da ta cewa kuma babu wanda ya isa ya taba Magu. Sai dai asalin abin da ya kawo rikicin shine daukaka karar da Gwamnatin Tarayya tayi kan binciken Shugaban Majalisar Bukola Saraki.

KU KARANTA: PDP ta soki Gwamnatin Shugaba Buhari

Babban dalilin da ya sa Sanatoci ke kokarin tsige Osinbajo

Majalisa na nema ta tsige Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo

2. Kasafin kudi

Haka kuma Ministan Tarayya Babatunde Fashola na ta cacar baki da Sanatocin kan kundin kasafin kudin bana. Fashola ya zargi Majalisa da badakala. 'Yan Majalisa na ganin Osinbajo bai ja masa kunne ba.

3. Kiranyen Dino Melaye

Sai kuma maganar koro Dino Melaye daga Majalisar wanda Bukola Saraki yake gani zai yi masu illa kwarai da gaske.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko za ka iya barin Najeriya zuwa wata kasa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel