Bamu yarda da tattaunawa da Osinbanjo yake yi ba - Samarin Ohanaeze

Bamu yarda da tattaunawa da Osinbanjo yake yi ba - Samarin Ohanaeze

-Kungiyar OYC ta soki tattaunawar da Osinbanjo yakeyi saboda rashin wakilcin samari

-Kungiyar tace kofan ta bude yake ga duk wanda ke son tattaunawa da su

-Rashin wakilcin samari a tattaunawar zai sa baza a samu nasara ba

Kungiyar samarin kabilar ibo mai suna Ohanaeze Youth Council worldwide, OYC a ranar Lahadi tace bata yarda da tattaunawar da mukadashin shugaban kasa Osinbanjo yake yi ba tare da wasu shugabanin arewa da kudu maso-gabashin Najeriya.

A wata sanarwa da kungiyar ta bada ta hannun sakataren kungiyan, Mr Obinna Adibe yace yin tattaunawan ba tare da samari ba, ba zai haifar da da mai ido ba.

Bamu yarda da tattaunawa da Osinbanjo yake yi ba - Samarin Ohanaeze

Bamu yarda da tattaunawa da Osinbanjo yake yi ba - Samarin Ohanaeze

Idan za’a iya tunawa tun bayan samarin arewan sun bada sanarwan cewa kabilar ibo su fice daga arewa, Osinbanjo yana ta zaman tattaunawa da shugabanin siyasa da na addini daga bangarorin guda biyu.

KUMA KU KARANTA: Sharhi: Yadda za'a iya kira Dino Melaye daga majalisar dattijai

Kungiyar tace maganar korar ya shafi samari, ya kamata a gayyace su a wajen tattaunawar.

Mun sa ido a kan duk tattaunawa da mukadashin shugaban kasan yakeyi da gwamnonin kudu maso gabashin kasan, da masu sarautan gargajiya, shugabnin kabillar ibo da kuma shugabanin arewa.

“Mun lura cewa a duk tattaunawar tasa da wadannan kungiyoyin, samari basu samu wakilci ba, wannan shi yasa muka gane tattaunawar baza tayi tasiri ba”, Inji Kungiyar

Kungiyar ta yaba ma gwamnonin jihohin kudu maso gabashin Najeriya, domin kwazo da hangen nesan su. Sun kuma yi kira da gwamnonin da su ci gaba da kokarin kiyaye dukiyoyi da rayyukan mutanen jihohin domin samun cigaban yankin.

A kan maganar korar kabilar ibo daga arewa, kungiyar tace kofan ta a bude yake domin tattaunawa saboda tashin hankali bashi da amfani.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel