A'aha: Wata mata tayi abin kwarai Gwamnati tayi mata na tsiya

A'aha: Wata mata tayi abin kwarai Gwamnati tayi mata na tsiya

– Kwanaki wata mata ta maidawa Gwamnati sama da Miliyan guda

– Sai dai yanzu Gwamnati ta hukunta ta ta bisa laifi

– Gwamnatin Jihar Kogi tace matar ta yi wa jama’a karya

Kwanaki wata Ma’aikaciyar Gwamnatin Jihar Kogi mai suna Husseina Muhammad ta maida sama da Miliyan guda da aka tura mata a asusu bisa kure.

A'aha: Wata mata tayi abin kwarai Gwamnati tayi mata na tsiya

Gwamnan Jihar kogi Yahaya Bello

Wannan mata da tayi wannan abin kwarai dai Gwamnati tayi mata na tsiya don kuwa an dakatar da albashin ta an kuma gargade ta da sunan ta fadawa Duniya labarin da ba shi ne ba. Ku na sane cewa albashin wannan Ma’aikaciya dai bai wuce N35, 000 a wata ba.

KU KARANTA: APC ta sha kashi a zaben Jihar Osun

Haka kuma an haramtawa wannan mata magana a Jarida ko ma a kara horas da ita. A wancan lokaci rokon ta a biya Mijin ta albashin sa da yake bin Gwamnatin Jihar na sama da shekara guda.

Hukumar INEC tace gobe Litinin za ta fara aikin koro Sanata Dino Melaye na Jihar Kogi daga Majalisa kamar yadda tayi niyya. Makon jiya ne Kotu tace a dakata da maganar na dan lokaci tukuna.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani Minista ya dace a sallama daga aiki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel