Dalilan da suka sa naki sauka daga kujerar shugaban Majalisa duk da shari'ar kotun CCT

Dalilan da suka sa naki sauka daga kujerar shugaban Majalisa duk da shari'ar kotun CCT

-Senata Bukola Saraki ya fadi dalilan da yasa bai sauka daga kujerar sa ba a yayin da kotun da’an mai’aikata ke gudanar da bincike a kansa

-Saraki yace masu adawa dashi suna adawa ne da ikon Allah domin Allah ne ya bashi mulkin

Shugaban majalissan dattawa Bukola Saraki yayi bayanin dalilin da yasa bai sauka daga kujerar sa ba a majalisan duk da matsi da takura da ya shiga.

Saraki ya bayyana cewa damuwa ya masa yawa sosai a lokacin da ake binciken amma ya kira wani Malami domin neman addua amma Malamin yace masa ya maida komi zuwa ga Allah.

Dalilan da suka sa naki sauka daga kujerar shugaban Majalisa duk da shari'ar kotun CCT

Dalilan da suka sa naki sauka daga kujerar shugaban Majalisa duk da shari'ar kotun CCT

NAIJ.com ta ruwaito cewa shugaban majalisan ya fadi wannan Magana ne a garin Ilorin da ke jihar Kwara a lokacin da yake ma magoya bayan sa jawabi.

KUMA KU KARANTA: EFCC tayi yunkurin a kan 'yan majalisa, tana yunkurin kama wasu Sanatoci

Kamar yadda jaridar Sun ta ruwaito, Sarakin ya gode ma magoya bayan nasa domin adduo’in da suke masa a lokacin da ake binciken.

Yace: “Lokacin da suka ce min inyi marabous, na tambaye su dalili? Mun san irin gwagwarmayar da muka yi kafin kafa wannan gwamnatin kuma kawai suna yaki ne da ikon Allah. Suna bakin ciki da abin da Allah keyi.

“Muna godiya ga Allah domin lokacin da wannan matsalan ta faru, mun hadu a wannan wurin kuma munce zamu sake haduwa a gaba, Kuma Allah ya kadara mun sake haduwa.

“Ina godiya ga Sarkin Illorin domin irin goyon bayan da ya bamu. Yayi kokari iya matuka har wasu sarukan kasan nan sun sani, daga baya ma cewa yayi mu maida al’amarin ga Allah duk da kuwa yana da ilimin aikin lauya.

“Ina son in mika godiya ta sosai ga iyayen mu mata. Da matsalar ta fara, kun rikice amma duk da haka kunyi iya kokarin ku domin ku taimake mu. Kuma kunyi taimakon ne saboda kauna da kuke man aba don siyasa ba.”

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel