Tubabbun 'yan Boko Haram 52 na samun horon wayarwa daga gwamnati a Gombe

Tubabbun 'yan Boko Haram 52 na samun horon wayarwa daga gwamnati a Gombe

- Wasu daga mayakan Boko Haram sun balle daga kungiyar

- Da yawansu sun tuba suna kuma neman ilimi

- A jihar Gombe ana wayar da kan tubabbu 52

A lokuta da dama, akan sami wasu da ke da ra'ayin tuba, daga cikin mayakan Boko Haram, kuma wannan yana zama wata hanya da zasu koma cikin iyalansu, cikin jama'a. A yanzu haka, ana wayar da kan mutane 52 a jihar Gombe wadanda suka tuba, kuma gwamnati ke musu shiri na musamman na makonni 16.

Tubabbun 'yan Boko Haram 52 na samun horon wayarwa daga gwamnati a Gombe

Tubabbun 'yan Boko Haram 52 na samun horon wayarwa daga gwamnati a Gombe

Tubabbun 'yan Boko Haram 52 na samun horon wayarwa daga gwamnati a Gombe

Tubabbun 'yan Boko Haram 52 na samun horon wayarwa daga gwamnati a Gombe

A lokacin bude taron, Bamidele Shafa, wanda shine shugaban shirin da aka yi wa lakabi da operation safe corridor, ya ce lallai wadannan samari zasu sami horo na zama 'yan kasa na gari, kuma za'a koya musu sana'ar hannu don samu damar rike kansu.

A yayin wannan atisaye da zasu samu, zasu sami shiri daban daban daga ma'aikatu da cibiyoyi na gwamnati domin su sake zama mutanen kirki.

KU KARANTA KUMA: Philip Effiong Jr. ya caccaki Nnamdi Kanu

Wannan dai wata hanya ce da za'a iya magance matsalar tsaro, idan dai masu tada kayar bayan suka ajje makamansu suka mika wuya, domin dai, ana ganin da yawansu yaudararsu akayi aka koya musu ta'addanci da zafin ra'ayi.

A yanzu dai, ya kara da cewa, za'a tuntubi iyalansu a tattauna dasu, domin samun saukin komawarsu gida.

A nasu bangaren Sale Muhammadu, shugaban wadanda suka dawo daga rakiyar ta'addanci, yayi godiya ga gwamnatin tarayya da ta karbe su, take kuma da niyyar taimakonsu, duk da irin ta'asar da suka tafka.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel