Kiris ya rage mu gama da Boko Haram, inji shugaban sojin saman Najeriya

Kiris ya rage mu gama da Boko Haram, inji shugaban sojin saman Najeriya

- Boko Haram sun dade suna kai hare-hare kauyuka

- An ci galaba akan yaki da Boko Haram

- Sojin suna kokarin samar da zaman lafiya a Kasa

Shugaban Sojin Saman Najeriya, Sadique Abubakar, yace kiris ya rage da su gama da yakin da ake da Boko Haram a Arewacin Najeriya.

Yace sojinsu sun yi galaba akan gidajen ‘yan ta’addan Boko Haram da dama a arewa maso gabas din Najeriya, sun kuma tabbatar da nasara na gab da samuwa.

Kiris ya rage mu gama da Boko Haram, inji shugaban sojin saman Najeriya

Kiris ya rage mu gama da Boko Haram, inji shugaban sojin saman Najeriya

Sojin Kasa suna kan hanyar cin yaki da ta’addancin da ke afkuwa a wasu garuruwa da arewa maso gabashin Najeriya.

A shekaru biyu da suka gabata, ‘yan ta’adda suna kai hare-hare kauyuka. Ana samun ‘yan kunar bakin wake da dama da suke tada tarzoma, amma yanzu suna iya kokarin su na ganin sun ci galaba akan su.

KU KARANTA KUMA: Hotunan tubabbun 'yan Boko Haram

Sojin Najeriya suna iya bakin kokarin su ganin sun kau da ‘yan tada kayar baya. Da ganin babu wata kungiya da take iko da wani sashe na kasar face Gwamnatin Kasa.

Malam Abubakar ya tabbatar da sojin zasu cigaba da tsare lafiyar Kasa.

A cewar sa, goyon baya ya dace a bawa sojin domin kokarin da sukeyi maimakon Allah wadai da wadansu suke akansu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel