2019: Dalilina na barin PDP na koma APC - Gwamna Murabus Martins Elechi na Ebonyi

2019: Dalilina na barin PDP na koma APC - Gwamna Murabus Martins Elechi na Ebonyi

- A da nace idan na bar PDP na bar siyasa, amma yanzu na kasa

- A watan Afrilu ne tsohon gwamna Martins Elechi ya bar PDP

- Ya ce PDP cike take da barayi

Tsohon Gwamnan jihar Ebonyi da ya tsero daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC ya bada dalilan da suka saka shi barin jam'iyyar tasa, inda ya ce jam'iyya ce ta barayi, da rashin tausayin talakka.

A yanzu dai, jirgin APC sai kara cika yake da sababbin 'yan jam'iyya daga PDP wadanda ke kokarin rabuwa da tabon sata da ake musu kallo a zamanin mulkinsu.

2019: Dalilina na barin PDP na koma APC - Gwamna Murabus Martins Elechi na Ebonyi

2019: Dalilina na barin PDP na koma APC - Gwamna Murabus Martins Elechi na Ebonyi

A nasa bangaren, Shugaban jam'iyyar ta APC John Odigie Oyegun, yayi farin ciki da zuwan Martins Elechi zuwa jam'iyyarsu a bikin karbarsu ranar Alhamishin nan. Ana dai ganin karbuwar jam'iyyar a yankunan gabashin Najeriya na iya zama wani abin alheri zai kai su ga cin zabuka masu zuwa.

KU KARANTA KUMA: Tubabbun yan Boko Haram cikin hoto

'A da, nace idan na bar jam'iyyar PDP to na bar siyasa kacokam, amma a yanzu naga babu mafita sai an dama damu domin yiwa jama'armu aiki.' Inji Martins Elechi.

A yanzu dai, saura kasa da shekara a fara zabukan fidda gwani a cikin jam'iyyun siyasa, don manyan zabuka.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel