Zaben Osun: PDP ta doke Jam’iyyar APC

Zaben Osun: PDP ta doke Jam’iyyar APC

– Hukumar INEC ta tabbatar da PDP tayi nasara a zaben Osun

– Dan PDP ya doke ‘Dan takarar Gwamna Aregbosola

– Jam’iyyar APC ta tsira da karamar Hukuma tal

Ademola Adeleke ya bada mamaki a zaben Sanatan Jihar Osun inda ya lashe kananan Hukumomi 9 cikin 10. Wannan abu dai ya ba Jama’a mamakin gaske.

Zaben Osun: PDP ta doke Jam’iyyar APC

Dan takarar PDP ya doke Jam’iyyar APC

Jam’iyyar PDP ce ta lallasa APC a inda ta ke da karfi a Yankin Yammacin Jihar Osun. Ademola Adeleke ya tika Mudashiru Hussain na APC wanda Gwamnan Jihar Rauf Aregbosola ya marawa baya a zaben.

KU KARANTA: Kwankwaso ya nemi Gwamnonin Arewa su tattauna

Zaben Osun: PDP ta doke Jam’iyyar APC

Gwamnan Jihar Rauf Aregbosola sun sha kashi

Kwanakin baya ne Sanatan Yankin ya rasu don haka aka sake zabe domin maye gurbin Marigayin. Mutane dai sun ba ‘Dan uwan Marigayin Adeleke kuri’a 97, 480 inda ‘Dan APC ya samu 66, 116.

Shi kuma Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose ya bayyana cewa Hukumar tsaro ta DSS na nema tayi masa sharri a kuma kama sa a rufe da laifin cin amanar kasa. Gwamnan ke cewa Gwamnatin APC da kokarin wannan makarkashiya

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Fafutukar Nnamdi Kanu da Biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel