Sarkin Musulmi ya dai-daita da Magajin Garin Sakkwato, Hassan Danbaba

Sarkin Musulmi ya dai-daita da Magajin Garin Sakkwato, Hassan Danbaba

- Sarkin Musulmi da Magajin Garin Sakkwato, Hassan Danbaba sun dai-daita tsakanin juna

- Sarkin Kano da na gwandu sun ce Sultan na Sakkwato na matsayinsa uba ne ga Hassan Danbaba

- Sultan Abubakar da Magajin Garin Sakkwato biyu sun amince su gafarta wa juna

Jikan marigayi Ahmadu Bello, Firimiyan Arewacin Najeriya, Hassan Danbaba, ya sulhunta da Sultan na Sakkwato, Saad Abubakar III.

A makon da ta gabata ne Sarkin Musulmi ya samu sabani da Magajin Garin Sakkwato Mista Hassan Danbaba a bainar jama’a inda Danbaba ya ajiye makaminsa a matsayin Magajin Garin Sakkwato.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar Sarakunan gargajiya na Kano, Muhammadu Sanusi I da kuma na Gwandu, Muhammad Bashar suka sulhunta mutanen biyu.

Sarkin Musulmi ya dai-daita da Magajin Garin Sakkwato, Hassan Danbaba

Magajin Garin Sakkwato, Hassan Danbaba, jikan marigayi Ahmadu Bello, Firimiyan Arewacin Najeriya Source: premiumtimesng

A yau Asabar, 8 ga watan Yuli ne sarakunan biyu suka isa fadan sarkin musulmi don su sulhunta Sultan Abubakar da Hassan Danbaba.

KU KARANTA: Matsin tattalin arziki: Maniyyata aikin hajji 30 suka kasa cika kudin su daga Daura

Masu shiga tsakani sun bukaci Magajin Gari da ya nema gafara daga Sultan saboda Sultan na Sakkwato yana matsayin uba ne a gareshi. A cewar majiyar.

A karshe kai shugabannin biyu sun yarda su gafarta wa juna.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel