Dan Tsohon Sojan Bayafara ya yi raddi kan Nnamdi Kanu

Dan Tsohon Sojan Bayafara ya yi raddi kan Nnamdi Kanu

- Nnamdi Kanu dai yayi kaurin suna wajen kambama batun kaa sabuwar Kasar Bayafara, ta kabilar Ibo, daga Najeriya, sai dai dan gidan Philip Effiong daga kabilarsa, mazan jiya, ya fadi ra'ayinsa kan sabon kokarin samarin yankin.

Da ga tsohon mataimakin Ojukwu a lokacin yakin Basasar Najeriya, Philip Effiong Junior, ya caccaki Nnamdi Kanu a matsayin dan koyo wanda bai san inda zai kai jama'ar kabilarsu ba, da burinsa na kafa kasar Bayafara.

Tsohon Sojan Bayafara ya yi raddi kan Nnamdi Kanu

Tsohon Sojan Bayafara ya yi raddi kan Nnamdi Kanu

Efiong, ya gaya wa BBC Africa cewa, sabon kokarin ya kara sayar da kabilar Ibo a kan abin da ake zarginsu, cewa basu da siki sai kabilanci da son mamaye Nayeriya a fagen siyasa da mulki.

KU KARANTA KUMA: Bukola Saraki ya gana da Osinbajo kan batun zargin tsige Farfesan

Dadin dadawa, yace banda asara babu wani abu da kokarin zai kawo wa kabilarsu. Amma ya ce shi ba zai kushe Nnamdi Kadu gaba daya ba, domin ya tuna lokacin da jiragen Najeriya ke ruwan bama-bamai a kan su a jihar Enugu.

A yanzu dai, Nnamdi Kanu shine shugaban kokarin kafa kasar Bayafara, kuma yana samun karbuwa daga yankin nasa, inda har 'yan siyasa suna shakkar tanka masa.

A bangarensu dai, magoya baya Nnamdi Kanu sunce bukulu ne ke sa wasu daga kabilar tasu suka ga Nnamdi Kanu, ganin yadda aka sami ci gaba wajen yada wa kabilar son kafa tasu kasar.

A watan Oktoba dai ake sa rai za'a ga me zai faru a harkar zabe a yankin, ko jama'a zasu bi umarnin kungiyar IPOB na kin kada kuri'a ko kuma a'a.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel