Matsin tattalin arziki: Maniyyata aikin hajji 30 suka kasa cika kudin su daga Daura

Matsin tattalin arziki: Maniyyata aikin hajji 30 suka kasa cika kudin su daga Daura

- Matsin tattalin arzikin kasar ya hana wasu zuwa makka

- Mutanen dai su 30 ne

- Mutanen yan asalin garin su Buhari ne

Sama da maniyyatan aikin hajin bana su talatin ne a karamar hukumar Daura ta jihar Katsina, suka amshi kudin ajiyar da suka fara ajiye naira miliyan daidai a bankuna, saboda rashin halin cika naira dubu dari biyar biyar da gwamnatin tarayya ta kayyade kudin hajin bana a kan naira miliyan daya da rabi.

NAIJ.com ta samu labarin cewa majiyar mu ta Katsina Postta rawaito mana cewa jami'in hukumar aikin hajin na karamar hukumar Alhaji Lawal Nababa shi ne ya bayyana haka a ranar Talatar da ta gabata.

Matsin tattalin arziki: Maniyyata aikin hajji 30 suka kasa cika kudin su daga Daura

Matsin tattalin arziki: Maniyyata aikin hajji 30 suka kasa cika kudin su daga Daura

Ya ce adadin da hukumar haji ta ware wa karamar hukumar Daura na Maniyyata 175, abun ya sami tasgaro a yankin.

Daura dai karamar hukuma ce a cikin jihar Katsina kuma daga nan ne shugaba Muhammadu Buhari ya fito.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel