Jonathan da wasu manyan jiga-jigan PDP sun je yin ta'aziyyar Maitama Sule

Jonathan da wasu manyan jiga-jigan PDP sun je yin ta'aziyyar Maitama Sule

- Ana ci gaba da kwarara Kano don ta'aziyyar Maitama Sule

- Jonathan da mukarraban sa sun je yau

- Jiga-jigan jam'iyyar PDP suna tare da Jonathan din yau

Tsohon shugaban Najeriya Cif Goodluck Ebele Jonathan tare da wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP ta kasa sun shirya tsaf domin zuwa Kano domin mika ta'aziyyar su ga iyalai, gwamnati da ma masarautar jihar kan rasuwar Maitama Sule, Dan Masanin Kano.

A yayin da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan suka hadu da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido da sauran wasu jiga-jigan PDP a filin jirgin sama na Abuja inda za su shilla Kano domin mika ta'aziyyar Danmasanin Kano.

Jonathan da wasu manyan jiga-jigan PDP suna shirin zuwa yin ta'aziyyar Maitama Sule

Jonathan da wasu manyan jiga-jigan PDP suna shirin zuwa yin ta'aziyyar Maitama Sule

NAIJ.com ta samu cewa daga cikin tawagar akwai Barista Kabiru Tanimu Turaki, Sanata Bala Muhammad, Kwamred Abba Morro, Dr. Akilu Indabawa da sauransu.

Muna addu'ar Allah ya sansayay makwancin sa. Amin.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel