Hukumar kula da aikin hajji ta kara wa'adin karbar cikon kudin zuwa hajji

Hukumar kula da aikin hajji ta kara wa'adin karbar cikon kudin zuwa hajji

- An kara daga lokacin rufe karbar cikon kudin hajji

- An kara lokacin ne da kwana 7

- Ana sa ran za'a fara tashi a 30 ga wannan watan

Hukumar kula da aiyyukan hajji ta gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugabanta Alhaji Abdullahi Muhammed ya umurci takwarorin sa na jihohin kasar nan da su kara lokacin da zasu rufe karbar cikon kudaden aikin hajji daga maniyyata zuwa kamar nan da kwanaki bakwai (7).

NAIJ.com ta samu labarin cewa Shugaban yace karin wa'adin ya wajaba ne bisa la'akari da yadda maniyyata da dama basu samu sun cika kudin nasu ba.

Hukumar kula da aikin hajji ta kara wa'adin karbar cikon kudin zuwa hajji

Hukumar kula da aikin hajji ta kara wa'adin karbar cikon kudin zuwa hajji

A cewar sa: “Aikin Hajji umarni ne kuma idaba ce, don haka a na mu bangaren ya zama wajibi mu tabbatar da cewa mutane sun samu saukin samun damar cika sauran kudin da ba su karasa cikawa ba.

Jiragen da zasu yi kwangilar daukar mahajjatan a bana dai sun hada da Max Air da kuma Medview haka zalika tare kuma da Azman Air.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel