Gwamnatin jihar nan ta Arewa ta samar da tan 110,000 na takin zamani don manomanta

Gwamnatin jihar nan ta Arewa ta samar da tan 110,000 na takin zamani don manomanta

- Gwamnan jihar Katsina yayi kokari

- Manoman jihar ta Katsina zasu dara

- Gwamnatin jihar ta siyo taki mai yawo domin manoman jihar

Babban sakataren ma'aikatar gona ta jihar Katsina Alhaji Idris Tine ya bayyana haka a lokacin da yake zagayawa da kwamishinan ma'aikatar noma na Jihar Katsina wanda kuma shine mataimakin gwamnan jihar Alhaji Mannir Yakubu a kamfanin samar da taki dake Funtua.

Alh Idris Tine ya bayyana cewa a halin yanzu an samar da sama da tan dubu 23 daga cikin tan dubu 50 da gwamnatin jihar za ta raba, sannan kuma za ta ci gaba da karbar tan dubu 6 daga cikin tan dubu 60 da gwamnatin tarayya za ta samar wa jihar.

Gwamnatin jihar nan ta Arewa ta samar da tan 110,000 na takin zamani don manomanta

Gwamnatin jihar nan ta Arewa ta samar da tan 110,000 na takin zamani don manomanta

NAIJ.com ta samu labarin cewa babban sakataren wanda ya yaba da kokarin Gwamnatin ya kara da cewa bayan an samar da takin a kowacce rumfar zabe za a kuma rarraba shi a cibiyoyin sayar da taki na gwamnatin jihar domin amfanar manoman Jihar.

Haka kuma babban sakataren ya zagaya da mataimakin Gwamnan da sauran jami'an ma'aikatar gona a cibiyoyin samar da taki da ke kananan hukumomin Safana da Bakori wadanda dukkanin su suna karkashin ma'aikatar ma'adainai ta jiha domin farfado da su.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel