Zaben 2019: Wasu yan Najeriya 54 sun sha alwashin tara ma Sule Lamido N50 biliyan don yayi yakin neman zabe

Zaben 2019: Wasu yan Najeriya 54 sun sha alwashin tara ma Sule Lamido N50 biliyan don yayi yakin neman zabe

- Wata kungiya ta nuna goyon bayan ta ga Sule Lamido

- Kungiyar tace zata tara masa kudin kamfe

- Kungiyar dai tana da mutane 54

Wata kungiya a Jihar Bauchi mai dauke da mutane hamsin da hudu (G54) sunyi yunkurin hadawa Dr Sule Lamido CON naira biliyan 50 domin tunkarar zaben dake tafe na dubu biyu da goma sha tara 2019, don fitowa shugabancin kasar nan.

Shugaban rukunin mutanen Usman Yusuf, da yake magana da yan jarida bayan gama zaman da aka tattauna a wani otel, Awalah otel dake jihar Bauchi, shugaban kungiyar Usman Yusuf ya bayyana sun kirkiri wannan ne don ceto Nijeriya daga halin da take ciki, da irin hasashe da sukayi don tunkarar zaben 2019.

Zaben 2019: Wasu yan Najeriya 54 sun sha alwashin tara ma Sule Lamido N50 biliyan don yayi yakin neman zabe

Zaben 2019: Wasu yan Najeriya 54 sun sha alwashin tara ma Sule Lamido N50 biliyan don yayi yakin neman zabe

NAIJ.com ta samu labarin cewa runkunin sunce sun zabi Sule Lamido a matsayin daya tilo da kasar nan take da buri akansa a zaben da za'ayi na shugabancin kasar a 2019.

Ya bayyanawa al'ummar Nijeriya da suka bawa Dr Sule Lamido CON hadin kai, domin irin burin da yake dashi ga al'ummar Nijeriya, don ganin ya farfado da matsin tattalin arziki da kasar nan take ciki, idan har aka zabeshi.

Ya sake bayyana Sule Lamido a matsayin mutum ne mai kaifin basira, da hangen nesa, wanda har Allah ya kaishi ga nasara al'ummar Nijeriya zasu gaskata abunda aka fada akansa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel