Zan sa kafar wando daya da Ibrahim Magu - Gwamna Abdulaziz Yari

Zan sa kafar wando daya da Ibrahim Magu - Gwamna Abdulaziz Yari

- Zan sa kafar wando daya da Magu inji Gwamnan jihar Zamfara

- Gwamnan ya ce shugaban EFCC na son cin zarafin sa

- Gwamnan yace zai dauki mataki

Gwamnan Zamfara wanda kuma yake zaman Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya watau Alhaji AbdulAziz Yari ya zargi shugaban hukumar nan dake yaki da cin hanci da rashawa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) na wucin gadi a turance, Malam Ibrahim Magu da takurawa Gwamnoni takwarorin sa gwamnoni inda ya yi barazanar kai kasarsa ga fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Gwamnan ya kuma musanta zargin da EFCC ta gabatar a kansa na cewa ya karkatar da Naira milyan 500 daga cikin kudaden tallafi da gwamnatin tarayya ta baiwa jihar.

Zan sa kafar wando daya da Ibrahim Magu - Gwamna Abdulaziz Yari

Zan sa kafar wando daya da Ibrahim Magu - Gwamna Abdulaziz Yari

NAIJ.com ta samu labarin cewa Gwamnan ya ce manufar EFCC ita ce kawai ta nunawa duniya cewa tana tuhumar wani Gwamna ba tare kuma da kwararrun hujjoji ba.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa kafofin yada labarai da damu sun ruwaito cewa Gwamnan ya karkatar da kudin jihar har na biliyoyin Nairori wajen yi wa kansa hidima.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel