Shugaban Hukumar EFCC ya ayyana masu agazawa Boko Haram da kudi

Shugaban Hukumar EFCC ya ayyana masu agazawa Boko Haram da kudi

- Shugaban Hukumar EFCC ya bada bayani kan masu satar kudin Najeriya

- Har yanzu dai majalisa bata tabbatar da shi ba

- Yana zargin barayin gwamnati da mikawa Boko Haram kudade

Shugaban Hukumar EFCC ya bada bayanan wadanda ke taimakawa Boko Haram da kudade, ya kuma ce su din ne dai ke ingiza batun ballewar Najeriya domin kafa kasar Bayafara.

Wannan babban zargi ne dai da ba'a san ko daga ina ya sami wadannan bayanai ba, sai dai shugaban bai fadi ko su waye ba.

Shugaban Hukumar EFCC ya ayyana masu agazawa Boko Haram da kudi

Shugaban Hukumar EFCC ya ayyana masu agazawa Boko Haram da kudi

A bayaninsa da ya bayar a taron da yake halarta a jihar Kano, yace hukumarsa ta gano cewa masu sace kudaden gwamnati sune suke baiwa masu rajin son kafa kasar Bayafara kudi.

Ya kara da cewa, su ne kuma suke tura wa kungiyar Boko Haram kudaden gudanar da ayyukansu, amma kuma bai kama sunan kowa ba.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ne zai lashe zaben 2019

Ibrahim Magu, a makon jiya, ya ce wadanda aka kama da laiin satar kudaden gwamnati kamata yayi a tura su dajin Sambisa inda Boko Haram ke kafa daularsu ta 'yan tawaye.

'Ina tabbatar muku da cewa, barayin gwamnati sune suke mikawa 'yan ta'adda kudi, daga Boko Haram har ma da 'yan kungiyar IPOB masu son kafa kasar Bayafara ta kabilar Ibo', inji Ibrahim Magu.

Ya kuma kara da cewa da shugaba Buhari da mataimakinsa Faresa Osinbajo na iya kokarinsu kan dakile satar kudaden gwamnati.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel