Yusuf Buhari ya kammala Digiri na biyu a Landan

Yusuf Buhari ya kammala Digiri na biyu a Landan

– Yusuf dan gidan Shugaba Buhari ya kammala karatu

– ‘Dan Shugaban kasar ya gama Digirin sa na biyu

– Yusuf ne kadai ‘Dan Shugaba Buhari namiji a Duniya

Mun samu labari cewa ‘Dan gidan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Yusuf ya kammala karatun sa a Jami’ar Ingila da ke Turai.

Yusuf Buhari ya kammala Digiri na biyu a Landan

Hoton Yusuf Buhari daga Facebook

Yusuf Muhammadu Buhari ya kammala karatun sa na Di-gir-gir kamar yadda wani abokin sa bayyana a shafin sa na Facebook.Kwanakin baya ne dai wasu ‘Ya ‘yan shugaban kasar su ka gama karatu a wata Jami’a a kasar Ingila.

KU KARANTA: Biyafara: Osinbajo yace bakn alkalami ya bushe

Yusuf ne kadaai ‘Dan Shugaba Buhari namiji a Duniya don kuwa ‘dayan ‘Dan shugaba Buhari ya rasu. Yusuf na yawan zama a gida Daura kamar yadda mu ka ji kuma mutum ne mai saukin kai matuka.

Yanzu haka Shugaban kasar na kwance a Birnin Landan da ke kasar Ingilar. Ko kwanan nan mai dakin sa Aisha Buhari ta kai masa ziyara.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon yadda wata mai burodi ta zama mai kudi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel