Wai harda sunayen 'yan uwana a jaddawalin sunayen masu yi min kiranye - Dino Melaye

Wai harda sunayen 'yan uwana a jaddawalin sunayen masu yi min kiranye - Dino Melaye

-Dino Melaye yace akwai sunayen kawunan sa guda biyu da dan uwansa a jaddawalin sunayen masu yi masa kiranye

-Dino Melaye ya zargi gwamna Bello da kara sunayen mutane a takardan kiranye

-Dino Milaye yace Gwamna Bello Bashi da ikon ya kore shi daga majalisa

Senata Dino Melaye da ke wakiltan yankin Kogi na yamma ya bayyana cewa akwai sunan dan Uwansa da kuma Kawunan sa guda biyu a cikin jeren sunayen mutanen da ke son ayi masa kiranye.

Senator Melaye ya fadi wannan maganan ne a yayin da yake hira da jaridar Sun, ya kuma kara da cewa ba’a taba samun gwamna mara kishin jama’a ba kaman gwamna Yahaya Bello a tarihin jihar Kogi.

Wai harda sunayen 'yan uwana a jaddawalin sunayen masu yi min kiranye - Dino Melaye

Wai harda sunayen 'yan uwana a jaddawalin sunayen masu yi min kiranye - Dino Melaye

Ya kuma kara nanatawa cewa gwamna Bello yayi yunkurin halaka shi so da yawa a baya, kuma yace Bello bashi da ikon ya kore shi daga majlisan dattawa.

Ya kuma kara nanatawa cewa gwamna Bello yayi yunkurin halaka shi so da yawa a baya, kuma yace Bello bashi da ikon ya kore shi daga majlisan dattawa.

KU KARANTA: Zargin tumbuke Osinbajo, Osinbajo da Bukola Saraki sun gana

Melaye yace, “Yahaya Bello bai jefa min kuri’a ba, kuma baya yankin da nake wakilta saboda haka bashi da ikon da zai sa ayi min kiranye daga majalisa'.

Bello ya zauna da mukaraban sa ne, sun kwashe suna daga rajistan INEC, sannan suka rubuta sunayen a cikin takardan kiranyen'.

“Kasan cewa akwai sunan dan uwana na jini a cikin takardan? Kasan cewa akwai sunnan kawonai ne guda biyu a takardan?"

“Kuma mun gano cewa akwai sunayen bogi da yawa a cikin takardan, har da mutanen da suka rasu ma duk an sa sunnan su a takardan'.

“A wasu lokutan, sunayen mutanen da ke takardan ya wuce yawan sunayen mutanen da sukayi rajistan zabe a rajistan hukumar INEC'. Ya kara da cewa.

Yanzu dai nan da kwanaki za'a sani ko Kotu zata bari a yi zaben mayar da Melaye gida cikin wata uku.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel