Hukumar DSS za tayi wa Ayo Fayose kamun da ba zai fita ba

Hukumar DSS za tayi wa Ayo Fayose kamun da ba zai fita ba

– Hukumar DSS na shirin damke Gwamnan Jihar Ekiti

– Gwamna Ayo Fayose ya bayyana hakan da kan sa

– Fayose yace ana kokari a ga bayan sa a huta

Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose ya bayyana cewa Hukumar tsarota DSS na nema tayi masa sharri a kuma kama sa a rufe da laifin cin amanar kasa.

Hukumar DSS za tayi wa Ayo Fayose kamun da ba zai fita ba

Hton Gwamna Ayo Fayose a Jihar Benin

Hukumar DSS ne ke shirin damke Gwamnan na Jihar Ekiti da sunan cin amanar kasa kamar yadda ya fada. Ko da dai babu wanda ya isa ya taba Gwamna har sai wa’adin sa ya cika amma idan ha aka same sa da wannan laifi yashiga hannu.

KU KARANTA:

Gwamnan ke cewa Gwamnatin APC da kokarin wannan makarkashiya domin a ga bayan sa don kuwa shi ne muryar da ke taka Shugaba Buhari a duk kasar. A cewar Gwamnan, za a hada kai da wasu ne domin a kauda sa.

Kwanaki dai Mai girma Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Peter Fayose ya kora duk Kwamishinonin sa kamar yadda mu ka samu rahoto. Mai taimakawa Gwamnan wajen yada labarai ta kafafen zamani Lere Olayinka ya bayyana haka.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel