Wasu 'yansanda sun yi awon gaba da Evans mai garkuwa da mutane, duk da cewa yana hannun 'yansanda

Wasu 'yansanda sun yi awon gaba da Evans mai garkuwa da mutane, duk da cewa yana hannun 'yansanda

- 'Evans mai garkuwa da mutane ya bata'

- Evans dai ya amsa cewa lallai yana sata da garkuwa da mutane

- A jihar Legas aka kama Evans amma ba'a ji duriyarsa ba

A halin yanzu da ake ciki,ba a san inda Kasungurmin mai garkuwa da mutane Chukwuduneme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans yake ba.

Amma wasu manyan ‘Yan Sandan suna zargin an fitar da shi daga hannun ‘yan Sandan Jihar Legas da tsakar dare, an kai shi Abuja.

An nemi Evans sama da kasa

An nemi Evans sama da kasa

Bayan zagaye da Jami’an ‘yan sanda suka yi tayi a Ofishin ‘yan Sandan a Legas, domin samun bayanin idnda Evans yake . Sun gano cewa an fitar da shi daga jahar ne amma ana gab da dawo da shi.

Iyalinsa suna tsoron ko ya mutu ne, amma labarai ya nuna yana nan da rai, sai dai ba a san takamaimai inda yake ba.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ne zai ci zabe a 2019

Wani mai kawo rahoto da ya ziyarcci jamian yan sandar ta Jahar an gaya mishi cewa an hana ‘Yan Jarida ganawa da Evans.

Jami’an’ Yan Sanda a satin baya sun sami Kotun da za ta rike shi tsawon wata uku don su sami isashen lokacin gama bincike akan sa. Bayan haka ne Evans ya kai karar su da su sake shi ya kuma yace sai an biya shi diyyar naira miliyan N300.

Wasu manyan Jami’an ‘Yan Sanda suna tsroron ballewar Evans daga hannun Kotu ko Kurkuku, ko kuma ya koma kan sana’arsa tare da ‘yan uwansa.

Rashin sanin takamaiman wurin da evans yake, ya sa wanda suka bi labarin tun daga diddigin kama shi cikin rudani . Wasu ‘Yan Sandan sun tabbatar yanzu haka Evans baya hannun hukumar ‘Yan Sandan Legas

Wata majiya tace’ An fitar da Evans ne domin cigaba da bincike da ake a kan sa,. Ba wanda yake da niyyar Kashe Evans, amma zasu dawo da shi bayan binciken. Amma akwai tabbacin Evans yana nan da ransa, koda wani abu ya faru da shi, ko ya mutu a hannun hukuma to ciwon dajin da yace yana tare da ita ne ta kasha shi.’

Evans yana nan tsare lafiya kuma yana bada hadin kai akan binciken da ake masa.

Har yanzu iyalinsa basu sami damar ganawwa da shi ba. ‘Yan uwansa da dama sun yi riba da kudaden da Evans ya samu. Don ya tabbatar ya saya wa baban sa mota ya kuma bashi kudi har naira milyan uku.

Sabon Karin Bayani: Hukumar Yansanda ta fitar da sanarwar cewa Evan bai bace musu ba, kawai dai ta boye shi ne saboda tsaro, da kuma hana shi magana da 'yan jarida.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel