Zargin tumbike Mukaddashin Shugaban Kasa: Saraki ya gana da Osinbajo

Zargin tumbike Mukaddashin Shugaban Kasa: Saraki ya gana da Osinbajo

- Saraki ya gana da Osinbajo

- Majalisar Dattijai tayi barazanar tumbike Mukaddashin Sugaban Kasa

- Majalisar tana so a bi dokokin da ta shimfida

Shugaban Majalisar Dattijai Dr. Bukola Saraki ya gana da Mukaddashin Shugaban Kasa Prof. Yemi Osinbajo a ranar Alhamis akan wasu maganganu da aka tattauna a majalisar na zargin tsige Mukaddashin Shugaban Kasa.

Bincike ya bayyana ganawar da Shugaban Majalisar yayi da Mukaddashin Shugaban Kasa akan zargin tsige Mukaddashin Shugaban Kasar ne. Saraki yayi wa Osinbajo bayani ne musamman akan zancen zargin yana so ya zama Mukaddashin Shugaban Kasa.

Zargin tumbike Mukaddashin Shugaban Kasa: Saraki ya gana da Osinbajo

Zargin tumbike Mukaddashin Shugaban Kasa: Saraki ya gana da Osinbajo

Akwai alamomi da suka nuna barzanar da majalisar take shiryawa wajen tumbuke Mukaddashin Shugaban Kasar.

Daya daga cikin su akwai musayar da take faruwa tsakanin Majalisar da Ofishin Shugaban kasa kan cigaban aikin Ciyaman din hukumar Yaki da CIn Hanci da Rashawa (EFCC) Ibrahim Magu. Majalisar ta tattaunawa akan dakatar da shawarar gabatar da cigaban Ciyaman din Hukumar (EFCC) Ibrahim Magu.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ne zai lashe zaben 2019

Wasu tsofaffin Shuwagabanni sun hada kai da Mukaddashin Shugaban Kasar kan barazanar da tsige shi daga mulki. Sun bawa Osinbajo baki kan ya mayar da hankalin shi kan aikin shi yayi watsi da duk wani abu da yake son janyo rikici a kasar. Kuma sun Jadadda masa goyon bayansu bisa mulikin sa.

Batun tsigewar ya faru ne akan wasu lamari da suka faru a cikin majalisar. Majalisar ta zabe kanta daga yadda da cigaban Ibrahim Magu a matsayin Mukadashin Hukumar EFCC.

A cewar Shugaban majalisar ‘Bazamu zartar da koka ba kuma muga ba a bin dokar, wannan lamari ne da yakamata a duba. Dole Mukaddashin Shugaban Kasa yabi dokokin da muka shimfida, sakamakon haka, zamu dau matakin da ya kamata.’

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel