Gwamnatin Jigawa ta kaddamar da hutu ga ma'aikatan Jihar

Gwamnatin Jigawa ta kaddamar da hutu ga ma'aikatan Jihar

- A ranar Juma’a 7 ga watan Yuli gwamnatin ta kaddamar da hutun.

- Ma’aikatan Jihar zasu damar yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari Addu’a

- Kungiyar DSS sunyi shirin hana zagon kasa da ake yiwa gwamnatin kasar nan

A ranar juma’a 7 ga watan Yuli gwamnatanin Jigawa ta kaddamar da hutun kwana daya ga ma’aikatan Jihar domin yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a.

A ranar Alhamis 6 ga watan Yuli kakakin shugaban mai’aikatan Jihar Alhaji Isma’il Ibrahim ya tabbatarwa da News Agency of Nigeria (NAN) wannan rahotan a babban birnin Jihar.

Ya ke cewa gwamnatin ta ba da hutun ne domin mai’aikatan su samu dammar yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a a kan rashin lafiyar da ya ke ta fama da ita da.

Gwamnatin Jigawa ta kaddamar da hutu ga ma'aikatan Jihar

Gwamnatin Jigawa ta kaddamar da hutu ga ma'aikatan Jihar

Ya kara da cewa gwamnatin tana shawartar al’umar Jihar das u dukufa a wannan babbar rana ta Juma’a domin yin addu’ar ga shugaban kasar ta mu da kuma marigayi Dan Masanin Kano da ya rasu a cikin wannan makon.

KU KARANTA: Sama da manema aiki 500 ne za'a tantance a jihar Kaduna

Rahotanni daga Sahara Reporters sun tabbatar da cewa hukumar DSS (Department of State Secret Service) sunyi yinkurin hana zagon kasa da ake yiwa gwamnatin kasar nan sakamakon rashin lafiyar da shugaba Muhammad Buhari yake fa ma da ita.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel