Masu nema a raba kasar nan ba su da hankali Inji tsohon Shugaban kasa

Masu nema a raba kasar nan ba su da hankali Inji tsohon Shugaban kasa

– Obasanjo yace ba zai so ganin an raba Najeriya ba

– Olusegun Obasanjo ke cewa masu wannan fafatuka ba su da hankali

– Tsohon shugaban kasar yace hakan ba zai gyara kasar ba

Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo yayi raga-raga da masu kira a raba Najeriya inda yace sun yi kuskure. Ko da dai tsohon Shugaban yace ya goyi bayan ayi wa Najeriya garabawul.

Masu nema a raba kasar nan ba su da hankali Inji tsohon Shugaban kasa

Hoton Tsohon shugaban kasa Cif Obasanjo daga NAIJ.com

Obasanjo yace sam ba raba Najeriya ce mafita ba inda ya alakanta matsalar kasar da mutanen cikin ta don haka ya nemi 'Yan kasar da su gyara halayen su. Cif Obasanjo ya nemi yan kasar su canza dabi’ar su.

KU KARANTA: Osinbajo ya rubutawa Inyamurai wasika

Masu nema a raba kasar nan ba su da hankali Inji tsohon Shugaban kasa

Hoton Masu nema a raba kasar nan daga NAIJ.com

Cif Olusegun Obasanjo a jawabin na sa da yayi a Legas yace ba zai so kasar ta rabe ba. Kwanan nan ne dai jagoran tafiyar Biyafara Nnamdi Kanu ya sha alwashin ganin bayan Obasanjo idan har ya taba sa.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ike Ekweremadu ya rubuta doguwar wasika ga mutanen da ke neman Kasar Biyafara inda ya kira su bi a sannu da fafutkar ta su.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Tafiyar masu yakin neman Biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel