Ai ka ji: Wani Ministan Shugaba Buhari ya shiga cikin matsala

Ai ka ji: Wani Ministan Shugaba Buhari ya shiga cikin matsala

- Minista Abubakar Malami ya wanke kan sa daga zargi

- An rahoto cewa Ministan ga barranta Gwamnatin Buhari daga kalaman Osinbajo

- Yanzu haka Ministan yace 'yan jarida ne su ka juya kalaman sa

Ministan sharia Abubakar Malami SAN yace 'yan jarida ne su ka juya kalaman sa amma ko kadan bai musanya maganganun Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ba.

Ai ka ji: Wani Ministan Shugaba Buhari ya shiga cikin matsala

Hoton su Minista Abubakar Malami daga NAIJ.com

Minista Abubakar Malami ya zargi 'Yan jarida da juya kalaman sa game da abin da Shugaban kasa na rikon kwarya Farfesa Osinbajo SAN ya fada kan shugaban Hukumar EFCC Mista Ibrahim Magu.

KU KARANTA: An yi kus-kus tsakanin Atiku da Shugabar wata kasa

Ai ka ji: Wani Ministan Shugaba Buhari ya shiga cikin matsala

Hoton taron Ministoci daga fadar Shugaban kasa

Da farko an rahoto cewa Ministan yace kalaman Mai girrma Yemi Osinbajo ba su da wani tasirin don kuwa ra'yin sa ne kurum ya fada. Fadar shugaban kasa ma dai ta wanke Ministan daga duk zargi kwanan nan.

Mai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin rashawa Farfesa Itse Sagay yace duk Ministan da ya ja da Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo a fili ayi waje da shi ba tare da wani daga kafa ba.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyo game da abin da ya kamata ka sani game da kasar waje

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel