Ka ji gargadin da wani babban Sanata yayi wa masu neman Kasar Biyafara

Ka ji gargadin da wani babban Sanata yayi wa masu neman Kasar Biyafara

– Sanata Ekweremadu ya rubuta doguwar wasika ga mutanen Yankin sa

– Ike Ekweremadu ya nemi Inyamurai su bi a hankali waje fafatukar Biyafara

– Hakan na zuwa ne dai bayan wasu sun hakinkance a raba Kasar

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ike Ekweremadu ya rubuta doguwar wasika ga mutanen da ke neman Kasar Biyafara inda ya kira su bi a sannu.

Ka ji gargadin da wani babban Sanata yayi wa masu neman Kasar Biyafara

Ekweremadu ya rubuta doguwar wasika ga Inyamurai game da Biyafara

A wata wasika da ke yawo da sunan Ekweremadu ya kira Inyamurai da su yi tunani game da batun neman rabewa daga Kasar wanda yace zai yi wahala kuma zai zo da cikas iri-iri na tattali da zamantakewa.

KU KARANTA: Yadda Biyafara ta faro a tarihi

Biyafara

Wasu sun hakinkance a raba Kasar nan

Babban Sanatan ya kawo misalan kasashen da su ka shiga matsala bayan sun rabe da kin tsiya. Ekweremadu ke cewa dai ana nunawa Inyamurai banbamci musamman a wannan Gwamnati ta Shugaba Buhari.

A makon jiya ne Shugaban matasan nan na Arewa yace maganar korar Inyamurai daga Yankin da sake. Shettima Yerima ne ya ba Inyamuran wa’adi na su bar Arewa kwanakin baya wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce kasar.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel