Hukumar kula da aikin Hajji ta kara wa’adin karbar cikon kudi a hannun maniyyata

Hukumar kula da aikin Hajji ta kara wa’adin karbar cikon kudi a hannun maniyyata

Rahotanni dake zuwa mmana sun nuna cewa, Shugaban hukumar kula da aikin Hajji ta Kasa, Abdullahi Muhammed, ya ba hukumomin aikin Hajji umurnin tsawaita wa’adin karbar cikon kudade daga hannun maniyyata zuwa nan da mako guda.

Abdullahi ya bada umarnin ne a filin jirgin Abuja a yayin da ya ke sa hannun yarjejeniya da kamfanonin jiragen da za su yi jigilar maniyyata a shekarar nan ta 2017.

A cewarsa karin wa’adin mako guda ya zama dole domin a kara bayar da dama ga dukkan maniyyatan da ba su samu damar cika kudin su ba. “Aikin Hajji umarni ne kuma idaba ce, don haka a na mu bangaren ya zama wajibi mu tabbatar da cewa mutane sun samu rangwame gurin cika sauran kudin da ba su karasa cikawa ba.”

Hukumar kula da aikin Hajji ta kara wa’adin karbar cikon kudi a hannun maniyyata

Hukumar kula da aikin Hajji ta kara wa’adin karbar cikon kudi a hannun maniyyata

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Sakkwato tayi babban rashi – KARANTA

Shugaban ya kuma jaddada yakinin da ya ke da shi cewa dukkan kamfanonin sufurin jiragen da za su yi jigilar maniyyata da kuma dawo da mahajjata gida, duk nagartattu ne, ba za su ba kasar kunya ba.

Daga nan sai ya yi kira ga jiragen sufurin da su hada kai a tsakanin su wajen yi wa kasar nan hidima a lokacin jigilar ta wannan shekara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel