An yi an gama: Babu maganar Biyafara Inji Fadar Shugaban Kasa

An yi an gama: Babu maganar Biyafara Inji Fadar Shugaban Kasa

– Farfesa Yemi Osinbajo yace za a shawo karshen maganar Biyafara

– Mukaddashin Shugaban kasa yace tun bayan yakin basasa aka ajiye maganar raba kasar

– Ya kuma sha alwashin za a sharewa masu kuka hawaye

Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya sha alwashin sharewa masu kuka hawaye game da maganar Biyafara.

An yi an gama: Babu maganar Biyafara Inji Fadar Shugaban Kasa

Hoto masu fafutukar Biyafara daga NAIJ.com

Farfesa Osinbajo yayi wannan magana ne ta bakin mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa Babafemi Ojodu. Fadar shugaban kasa tace maganar Biyafara babu ita don an gama wannan batu tun lokacin Yakin basasa.

KU KARANTA: Kalmar Buhariyyah ta shiga kamus

An yi an gama: Babu maganar Biyafara Inji Fadar Shugaban Kasa

Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo

Yemi Osinbajo yace burin sa ace kowane Dan Najeriya zai wayi gari ba tare da rasa abin da zai ci ba. Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo yayi raga-raga da masu kira a raba Najeriya inda yace sun yi kuskure ya nemi ‘Yan kasar su canza halin su.

Kun ji cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Dr. Ike Ekweremadu ya rubuta doguwar wasika ga mutanen da ke neman Kasar Biyafara inda ya kira su bi a sannu.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko za ka iya barin Najeriya [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel