Saminu Turaki zai shafe kwanaki 77 tsare a hannun EFCC

Saminu Turaki zai shafe kwanaki 77 tsare a hannun EFCC

- Hukumar EFCC zata ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Jigawa har tsawon kwanaki 77

- Wannan ya biyo bayan kamun da suka yi masa a wajen wani taro da aka gabatar a Abuja

- Kwanaki 77 din ya yi daidai da ranar komawa kotu don ci gaba da sauraron tuhumar da ake yi ma Samunu Turaki

Rahotanni sun kawo cewa hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa wato EFCC zata ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Jigawa, Samunu Turaki har tsawon kwanaki sabain da bakwai (77), bayan kama shi da hukumar ta yi a gurin taron kaddamar da littafin rayuwar Birgediy Zakariya Maimalari, wanda aka gudanar a ranar Talata, a cibiyar Shehu Yar’Adua dake babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Sakkwato tayi babban rashi – KARANTAGwamnatin jihar Sakkwato tayi babban rashi – KARANTA

Hukumar ta EFCC zata ci gaba da tsare shi har zuwa ranar 19 ga watan Satumba, wanda ya yi daidai da ranar da alkalin babban kotun tarayya dake Dutse ya tsayar a matsayin ranar komawa kotu don ci gaba da sauraran karar tuhumar da akeyi ma tsohon gwamnan.

Saminu Turaki zai shafe kwanaki 77 tsare a hannun EFCC

Saminu Turaki zai shafe kwanaki 77 tsare a hannun EFCC

Idan dai baza ku manta ba tun a ranar 3 ga watan Maris na shekarar 2013 ake wasan buya a tsakanin tsohon gwamnan na jihar Jigawa da jami’an hukumar EFCC, bayan alkali Sabi’u Yahuza ya ba da umurni ga sufeto janar nay an sanda da kuma hukumar EFCC kan cewa su kamo Turaki sannan su gurfanar da shi a gaban sa a duk inda suka gan shi.

Wannan umarni na alkali Yahuza ya biyo bayan irin yadda Turaki ya dade ya na kin halartar shari’ar sa da ya rika yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel