Da walakin: Majalisa tayi kokarin nada Bukola Saraki a matsayin Shugaban kasa

Da walakin: Majalisa tayi kokarin nada Bukola Saraki a matsayin Shugaban kasa

– Sanatocin Najeriya sun yi wani yunkuri a harkar siyasar kasar dazu haka

– An dai yi kokari a nada Bukola Saraki a matsayin Mukaddashin Shugaban

– Mukaddashin Shugaban kasar Farfesa Osinbajo yayi tafiya wajen kasar ya dawo

Daga fitar Osinbajo wajen Najeriya Sanatoci sun yi kokarin nada Saraki Shugaban kasa na rikon kwarya dazu. Wasu Sanatoci ne su ka kawo wannan kuduri sai dai tuni Saraki yayi watsi da maganar.

Da walakin: Majalisa tayi kokarin nada Bukola Saraki a matsayin Shugaban kasa

Hoton Mukaddashin Shugaban kasa wajen taro daga AU

Wani Sanatan Jihar Abiya Eyinanya Abaribe ya fara kawo magana a Majalisa cewa babu Shugaban kasa a Najeriya yanzu haka ganin cewa Mukaddashin Shugaban kasar yayi tafiya zuwa kasar waje domin taron AU na Afrika.

KU KARANTA: An nada sabon Kakaki a Majalisar Kano

Da walakin: Majalisa tayi kokarin nada Bukola Saraki a matsayin Shugaban kasa

Hoton Bukola Saraki tare da Mukaddashin Shugaban kasa daga Aso Villa

Tuni dai Sanata Kabiru Marafa wanda a da ba ya ga maciji da Bukola Saraki yace ai sai a nada Shugaban Majalisar Dattawan kasar wanda shi ne na 3 a matsayi ya dare kujerar kafin dawowar Shugabannin kasar.

Kwanan ne dama aka ga fasocin Bukola Saraki na takarar Shugaban kasa a Garin Ilorin. Tuni dai Mukaddashin Shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya dawo daga tafiyar da yayi.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko 'Yan Najeriya sun fara gajiya da mulkin Buhari?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel