Daliban firamare 6 daga arewa zasu wakilci Najeriya a kasar Czech

Daliban firamare 6 daga arewa zasu wakilci Najeriya a kasar Czech

Dalilan makarantun firamare shidda yan asalin jihar Katsina zasu wakilci Najeriya a wata gasar muhawara da za'ayi a ta kasa-da-kasa a can kasar Cec wadda ake yi wa lakani da Hearts of Europe international debate a turance.

Daliban dai a zabe su su wakilci kasar Najeriyar ne bayan da suka lashe wata gasar da akayi a shekarar da ta gabata a jihar Neja dake arewacin Najeriya.

NAIJ.com ta samu labarin cewa a yayin da yake bankwana da daliban a wajen wani taron da aka shirya musu, shugaban hukumar ilimi ta bai daya watau SUBEB Alhaji Lawal Buhari Daura ya ce Gwamna Aminu Bello Masari tuni ya amince da a fidda zunzurutun kudi har N21 miliyan don daukar nauyin yaran da ma dukkan wadanda za su tafi tare da su.

Daliban firamare 6 daga arewa zasu wakilci Najeriya a kasar Czech

Daliban firamare 6 daga arewa zasu wakilci Najeriya a kasar Czech

Daga nan ne kuma sai shugaban hukumar ya hori daliban da su nuna kwazo wajen muhawarar sannan kuma ya kalubalance su da su karewa jihar martabar ta da aka santa da ita ta hanyar samo nasara a gasar.

Haka nan kuma Alhaji Lawal Buhari ya yaba da kokarin da kuma kwazon malaman yaran ganin yadda suka horar da yaran yadda za su tunkari gasar.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel