Duk Ministan da yayi wa Osinbajo rashin kunya zai gane ba shi da wayau - Inji Farfesa Sagay

Duk Ministan da yayi wa Osinbajo rashin kunya zai gane ba shi da wayau - Inji Farfesa Sagay

- Farfesa Itse Sagay ya nemi a Hukunta duk Ministan da yayi wa Osinbajo rashin kunya

- Haka kuma yake cewa babu wanda ya isa ya taba Ibrahim Magu

- Wannan ya zo ne bayan abin da ya faru da Minista Abubakar Malami

Mai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin rashawa Farfesa Itse Sagay yace duk Ministan da ya ja da Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo a fili ayi waje da shi ba tare da wani daga kafa ba.

Duk Ministan da yayi wa Osinbajo rashin kunya zai gane ba shi da wayau - Inji Farfesa Sagay

Osinbajo tare da Farfesa Sagay daga NAIJ.com

KU KARANTA: Osinbajo ya kai ziyara gidan Marigayi Maitama

Sagay ya na maida martani don a baya an rahoto cewa Ministan sharia Abubakar Malami SAN ya barranta Gwamnatin Buhari daga kalaman Farfesa Yemi Osinbajo a kan Ibrahim Magu na Hukumar EFCC.

Duk Ministan da yayi wa Osinbajo rashin kunya zai gane ba shi da wayau - Inji Farfesa Sagay

Hoton Ministan Buhari watau Abubakar Malami

Farfesa Sagay yace game da batun Magu na EFCC kuma an gama magana tun bayan da Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yace ba za a tsige sa ba kuma ta zauna a hakan.

Dazu kun ji cewa Ministan sharia Abubakar Malami SAN yace 'yan jarida ne su ka juya kalaman sa amma ko kadan bai musanya maganganun Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ba.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Fafutukar Biyfara kawo yanzu [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel