Kotu ta yi barazanar daure Shugaban jam’iyyar APC Oyegun da sakataren sa

Kotu ta yi barazanar daure Shugaban jam’iyyar APC Oyegun da sakataren sa

Wata babban kotu a jihar Ebonyi, ta yi barazanar kama babban jigo kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, John Oyegun da sakataren sa, Mai Mala Buni sakamakon kin bin umurnin kotu.

Alkalin kotun H. A. Njoku ne ya yi wannan barazana inda yay a zama dole su gurfana a gaban kotu a ranar 28 ga watan Satumba domin bayar da gamsasshen bayani kan hujjar su na kin bin umurnin kotu da sukayi a rikicin shugabancin jam’iyyar a jihar Ebonyi.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Sakkwato tayi babban rashi – KARANTAGwamnatin jihar Sakkwato tayi babban rashi – KARANTA

Kotun ta fusata ne sakamakon kin bin umurninta da Oyegun da Mala Buni suka yi, bayan kotu ta dakatar da su daga yin wani canji a cikin shugabannin zartarwar jam’iyyar na jihar ta Ebonyi.

Kotu ta yi barazanar daure Shugaban jam’iyyar APC Oyegun da sakataren sa

Kotu ta yi barazanar daure Shugaban jam’iyyar APC Oyegun da sakataren sa

Rikici ya barke ne jam’iyyar APC reshen Ebonyi bayan Oyegun ya aika wa mataimakin shugaban jam’iyyar na jiha, Eze Nwachukwu wasikar cewa an daga matsayinsa zuwa mukamin shugaba.

Ganin haka, ne ya sa shugaban jam’iyyar, Ben Nwobasi, ya bayyana cewa shi bai amince a dakatar da shi ba, kuma sabon shugaban da aka nada, haramtaccen shugaba ne.

Wannan sa-toka-sa-katsi dai ta samo asali ne tun cikin 2014.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel