Wani sautin murya na a tada yaki a watan Oktoba na yawo a yanar gizo da wayoyi

Wani sautin murya na a tada yaki a watan Oktoba na yawo a yanar gizo da wayoyi

- Hukumomin Najeriya na kememe kan kamo masu son tada fada

- Kungiyar samarin arewa ta zame tace ba hannunta a wannan kira

- Sautin muryar na kira da a kashe da kone kabilar Ibo mazauna Arewa a watan Oktoban bana

Wani sautin murya mai tada hankali, cikin harshen Hausa, da ke yawo a wayoyin salula da sauran dandali na yanar gizo, na nan na yawo tsakanin jama'a a arewacin Najeriya, wanda ke kira ga samari da su tashi su kone dukiyar kabilun Ibo mazauna Arewa.

Wani sautin murya na a tada yaki a watan Oktoba na yawo a yanar gizo da wayoyi

Wani sautin murya na a tada yaki a watan Oktoba na yawo a yanar gizo da wayoyi

A cikin muryar dai, mai maganar ya bada sunansa a matsayin Ibrahim Jajere, wanda ya nuna yana zama a jihar Kaduna, ya ce kamata yayi a tada yaki na kabilanci kan kabilar Ibo, saboda kawai ya tsane su.

KU KARANTA KUMA: Bukola Saraki zai ceto Dino Melaye daga tsigewa

Da gani dai, wannan ja'iri, bashi da cikakken ilimi, hankali, da ma tarbiyya ko tausayi, domin ya nuna tsagwaron rashin imani, da rashin tausayi inda yake kira da a tada yaki domin wai tsarkake arewa.

'Kada ku taba dukiyar Yarabawa, su mutanen kirki ne, kada ku taba bayarabe, amma ku kone Ibo da dukiyarsu domin bassu d amfani' Muryar ta yi kira.

Ya kara da cewa basu bukatar makamai, wai ashana kawai suke bukata, domin wannan danyen aiki.

Kungiyar samarin arewa dai da a da tayi kira a kori kabilar Ibo, tace bata tare da wannan ja'iri, kuma ta ce kada a biye masa.

Ko hakan na nufin akwai abun tsoro dake zuwa cikin watanni biyu a arewa, ko kuma a'a? Sai mu zuba ido.

Ya zuwa yanzu dai, babu wata hukumar tsaroda ta kama wani cikin masu kokarin balle Najeriya ko tada yaki na kabilanci. Duk da a jihohi da yawa irin hakan har ta fara faruwa, a jihar Taraba da Kuros Ribas.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel