Yan kunar bakin wake 3 sun hallaka a jami’ar Maiduguri

Yan kunar bakin wake 3 sun hallaka a jami’ar Maiduguri

Yan kunar bakin wake 3 sun hallaka yayinda sukayi kokarin kai hari jami’ar Maiduguri jiya Alhamis, 6 ga watan Yuli.

Wata majiya ta bayyanawa jaridar TheCable cewa 2 daga cikin yan kunar bakin waken sun tayar da Bam ne a cikin jami’ar yayinda aka harbe daya wanda ke kokarin arcewa.

Wani jami’in tsaron jami’ar, Bashir Adam, ya tabbatar da wannan rahoto inda yace ta auku ne misalign karfe 11:30 na dare.

Adam yace yan Boko Haram din sun kawo hari bayan sun shigo jami’ar ta wani Katanga.

YANZU-YANZU: Yan kunar bakin wake 3 sun hallaka a jami’ar Maiduguri

YANZU-YANZU: Yan kunar bakin wake 3 sun hallaka a jami’ar Maiduguri

Yace da wuri jami’an tsaron jami’ar suka farga lokacin da sukaji karan tashin Bam kuma daya daga cikinsu na kokarin arcewa.

“Da farko mun harbeshi a hannun ne sannan muka karasahi lokacin da yake kokarin hayewa Katanga.”

“Dukkan yan kunar bakin wake sun mutu.”

KU KARANTA: Shin Atiku na shirye-shiryen 2019 ne?

Bunu Grema, wani mazaunin jami’ar yace yan ta’addan basu san makaranta ta tafi hutu ba.

Yace: “ Sun kai hari dakin kwanan dalibai ba tare da sanin cewa suna hutu ba. Mung ode Allah da basu kashe kowa ba.”

Tun ranan da aka sako yan matan Chibok 82 ne hare-haren Boko Haram ya fara yawaita a jami’ar Maiduguri.

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/?business_id=663027310546163&ref=page_internal#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel