‘Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 14 a jihar Rivers

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 14 a jihar Rivers

Wasu ýan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 14 a hanyarsu ta zuwa Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers daga Warri, jihar Delta, bayan haka sun nemi a basu kudi naira miliyan daya a mastayin kudin fansar ko wani mutun guda. Kenan suna bukatar naira miliyan goma sha hudu.

An sace fasinjojin ne a cikin wata motar bas wanda ke daukar mutane goma sha hudu na shahararren kamfanin sufurin nan wadda baá bayyan sunan ta ba.

Ýan bindigar sun tisa keyar dukkan fasinjojin motar tare da direban dake tuka motar. Jami’an tsaron na kamfanin motar sun gano motan a wurin da abun ya faru.

Masu garkuwan sun nemi iyalan kowanne daga cikin fasinjojin inda suka nemi kudin fansa daga gare su.

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 14 a jihar Rivers

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 14 a jihar Rivers

Sai dai bayan tattaunawa masu garkuwan sun rage kudin fansar zuwa naira dubu dari-dari.

KU KARANTA KUMA: An dakatar da Shugaban hukumar NHIS, kan zargin aikata zamba

A yanzu haka jamián tsaro sun fara gudanar da bincike kan alámarin sannan sun bad a tabbacin gano wadannan mutane da aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya.

Sannan itama kamfanin motar na iya bakin kokarinta don ganin an gano wadannan mutane.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Delta, CP Zanna Mohammad Ibrahim ya tabbatar da faruwan hakan inda ya ke cewa abun ya faru ne a Rumoji, jihar Rivers.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan

PDP ba zata taba dawowa karagar mulki ba – Lai Mohammed ga Jonathan
NAIJ.com
Mailfire view pixel