BINCIKE: Kwanaki goma kawai akayi ana ciyar da dalibai a jihar zamfara –Daliban suna roko da ayi musu kari

BINCIKE: Kwanaki goma kawai akayi ana ciyar da dalibai a jihar zamfara –Daliban suna roko da ayi musu kari

  • Kwanaki goma akayi ana ciyar da daliabai a jihar Zamfara
  • .Dalibai sun karu a lokacin da ake ciyarwa
  • Gwamnatin tarayya tace an ci gaba da ciyarwa ,makaratun kuma sun karyata

BINCIKE: Kwanaki goma kawai akayi ana ciyar da dalibai a jihar zamfara –Daliban suna roko da ayi musu kari.

BINCIKE: Kwanaki goma kawai akayi ana ciyar da dalibai a jihar zamfara –Daliban suna roko da ayi musu kari.

Kungiyar ciyar da abinci da aka kaddamar 2016,dan ganin yara suna zuwa makaranta dan rage tallace-tallace, da aikace-aikace sunyi bincike dan su gani. Shin sun cin ma manufofinsu? An samu cigaba.Femi Awolabi ya ziyarci kananan hukumomi guda bakwai a jihar zamfara dan binciken ayyukan. Amma bincike da yayi ya ja cecekuce a wajen jamaa .

Maryam musa yar shekara 7 da ke aji daya a makarantar Mareri model primary school a Gusau jihar zamfara ta rage sun makaranta tunda suka dawo daga hutu.

Maku biyu bayan an dawo makaranta a zangon karatu da yagabata. jin dadin karatu da son zuwa makaranta ya karu a zukatan dalibai. Musa da kawayenta suna jin dadin zuwa makaranta yanzu. Saboda ciyar da daliban makaranta da akayi ko wani rana wanda yana da ga cikin baban manufar gwamantin APC da sukayi alwashin yi a wajen yakin neman zabe.

KU KARANTA: Wani ministan shugaban kasa ya shiga matsala

Acikni cigaban da ake sa ran za asamu ya ta,aalaka akan abubuwa guda hudu ne .mukkadishin shugaban kasa prof Yemi Osinbanjo wanda aikin ciyarwa yana karkashin offishin sa ya lissafta abubuwan Kaman haka. Za a samu raguwan yara da suke fita da makaranta a frimari wanda yakai kashi 30% nay an makaranta,kuma tallace-tallace da aikace-aikace da kananan yara kai yi zai ragu .

Acikin N6 trillon na kasafin kudi shekara 2016 N93.1billion aka cire daga cikin N500billion na karfafa matasa da wa yanda basu da aiki dan ciyarwa.

Amma yanzu yan makarantar mareri model primary school Gusau na jihar zamfara sun daina samun shikafa da wake ranar litinin, babu alala da kunu ranar talata, babu doya ranar laraba, babu kunnu ranar alhamis kuma babu faten dankali wanda Mariam Musa tafi so ranar jumaa.

Makarantar babu dadi yanzu; Musa, tana cikin daliban da suka rage a makarantar bayan an daina ciyarwa.ta gaya ma majiyan cable

Kwanaki goma kawai akayi ana ciyarwa a jihar zamfara, amma ana sa ran za a cigaba da ciyarwa nan gaba.

AN RAGE MUN NAUYI KAFIN AKA DAINA CIYARWA

Lokacin farinciki ne ma Sa’adatu Abdullahi, bazawara mai yaya biyar.wanda wani juma’a a zangon karatu da ya gabata. yayanta suka shiga makarantar Ibrahim Gusau model school suka dawo gida cikin koshi.tun da ta rasa mijinta shekarun da suka gabata ciyar da yayanta yaza baban nauyi ga manta da aikinta shine yin kitso

Da safe ina basu N20 na kari amma nasan baya isan su baya iya siyan musu abinci ko kwano daya.

Nayi farinciki sosai kuma nauyi ya rage mun da gwamanti suka fara ciyar da yara a makaranta. Kafin ta tashi daga barci yayanta sun tashi har sun shiryawa makaranta dan su samu abincin kari.

Zainab zata tashi tayi shirin zuwa makaranta har ranar asabar;karmar yar Saadatu Abdullahi.

Abubuwan sun canza ma saadatu Abdullahi tunda aka daina ciyarwa ,yanzu yayanta suna dawowa gida da yunwa.damuwar ya karu sosai akan karamar yanta Zainab wanda ta daina zuwa makarata akulllun.

Ina cikin matukar farin ciki lokacin da ake bamu abinci a makranta ”inji Zainab yar aji biyu.

YANZU INA ZAMA A GONAR BABATA

Abdulrahman yaro dan aji biyar mara jin Magana.a lokacin da ake ciyarwa wanda ya kunshe aji daya zuwa aji uku banda yan aji biyar .Abdulrahman sai yasan yanda yashiga cikin yan kananan yara ya samo abincin.

Tunda ake daina ciyarwa na daina zuwa makaranta. Nafara zuwa gona ina taimakon babata Abdulrahman yagaya ma majiyan cable

DAN ALLAH, YAUSHE GWMANATI ZATA KAWO MANA NAMU ABINCIN

A lokacin da wasu makarantu suke jin dadin ciyarwa kafin a daina. Danbaza model primary school maradu. Sunce basu san anyi ba

Matamaikin shugaban makarantar ”Umar Sani, ya fadama majiyar cable’, munji batun ciyarwa har yanzu ba’a zo makarantar mu ba. Har wani lokaci ma wani mota a cike da abinci ya shigo makarantar a bisa kuskure yara suka taru dan cin abinci ya juwa ya fita a guje.

Makaratu da dama sun nemi ayi musu bayyani kan ciyarwar da akayi na kwana goma bai kai wajen su ba. Wani majiya ya gaya masu cewa mugayin yan siyasa aka ba kwangilan aikin ciyarwan.

Naji Kaman an cuce ne inji Nusaiba yar aji daya na Danbaza Model primary school.ta daga kai tana kallon majiyar cable,sai ta tambayeshi” wai dan allah yaushe gwamnati zata kawo mana namu abincin

ZUWA DA SHIGA MAKARANTA YA RAGU

Tunda gwamanti ta daina ciyarwa. Dalibai su ka daina zuwa makaranta.

A lokacin da gwamanti ta ciyar da dalaibai na kwana goma an samu dalibai sama da 267 amma yanzu da aka daina ciyarwa da kyar ake samun dalibai sama da 30.

Mallamin makarantar ya nunacewa sunyi yunkurin ganin daliban sun dawo. amma iyayensu sun mai dasu aiki a gonakinsu.

Shugaban makarantan Yahaya Hassan yace mallaman makarantan sun daina zuwa saboda babu dalibai da za’a koyar.

Yace sai an dawo da ciyarwan kafin dalibai su dawo.yace a satin na farko da aka fara ciyarwan abin farinciki ya faru saboda sama da dalibai 119 suka shiga makarantar. Ammma yanzu duka sun gudu. Ganin dalibai dayawa a makaranta na yana sani farin ciki sosai

HAR YANZU DALIBAI MAKARANTA NA ZUWA DA KWANAN ABINCI MAKARATA.

Har yanzu akwai daliban dake zuwa da kwanan abinci makaranta da sa ran ciki gaba da ciyarwa bayan an dakatar.

Musa Dalkurma shugaban makarantar yayi bayyani cewa. Yanzu suna fuskanta matsaloli na rashin lafiya daga dalibai Kaman ciwon ciki da ciwon kai. Amma lokacin da akai ciyarwa babu wannan matsalolin.

Tunda yanzu babu abinci ko magani dole ake barin dalibi yakoma gida hakan ya saba ma doka na rashin barin dalibi yakoma gida har sai an tashi daga makaranta.

Sadiq Ibrahim dan aji biyu ya daina zuwa makaranta dan karatu sai dai yazo ya sayar ma da dalibai mangwaro a N5. Ba zai taba tunanin sayar da mangwaro ba a lokacin da ake ciyarwa. mahaifiyarsa ke kawo masa mangwaro daga gona don ya sayar a makarantar

MASU KAWO ABINCI SUN DAINA ZUWA,YAN SIYASA SUN CINYE KUDIN.

N188,765,500M aka fitar dan ciyar da dalibai 269,665 masu da dafa abinci 2,738 a jihar zamfara Laolu Akande babban mataimakin mukkadshing shugaba kasa yace febrairu 2017 yace kudaden na ciyar da dalibai na kwana goma

Ba duka masu kawo abinci suka kawo ba. kuma wasu basu bada abincin har na kwana goma. wasu kwanaki hudu, wasu biyar wasu basu ma kawo ba kwatakwata.

Yayin da majiyan the cable sukayi Magana da wani mallamin makaranta. Ya fada musu cewa rashin biyan masu kawo abinci yasa basu kawo abinci ba. Hakan ya faru ne saboda gurbatattun yan siyaysa da aka ba kwangilan ciyarwar kuma suka handame kudaden.

LAOLU AKANDE

Akande yace ana cigaba da ciyarwa a jihar zamfara.

An dan dakatar ne saboda matsalar da aka samu daga banki weajen biya masu da abincin. Yanzu an kara wasu banuna biyu saboda a samu a biya kudaden da wuri.

Wasu shuwagbanin makarantu guda biyu sun ce har yanzu dai suna sa ido su gani ko ciyarwa zai kai makarantarsu.

A cikin shuwgabanin makarantun guda 10 da majiyan the cable ta tambaya dan tabbatar da maganar Akande, daya ne a karamar hukumar Shinkafi yace an sanar dashi cewa ciyarwa na makaratun zai cigaba.

https://business.facebook.com/naijcomhausa/?business_id=663027310546163#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel