Shirye shiryen 2019? Atiku ya halarci taron jam’iyya mai mulki ta ƙasar Ingila (HOTUNA)

Shirye shiryen 2019? Atiku ya halarci taron jam’iyya mai mulki ta ƙasar Ingila (HOTUNA)

- Tsohon shugaban kasa ya kai ziyara kasar Birtaniya

- Atiku Abubakar ya samu ganawa da shugaban kasar Birtaniya

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya samu ganawa da Firami Ministan kasar Birtaniya, Uwargida Theresa May a yayin taron jam’iyyar Conservative na kasar.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Atikun kansa, inda ya bayyana haka a shafinsa na kafar sadarwar zamani, Tuwita, kamar yadda NAIJ.com ta gano.

KU KARANTA: Allah wadai: Ya hallaka matarsa, bayan ya danƙara ma ýar aikinta ciki

A yayin taron walimar, Atiku ya sake yin watan ganawa da dan majalisar dokokin kasar Birtaniya, Liam Fox, kamar yadda ya shaida a shafin nasa na Tuwita.

Shirye shiryen 2019? Atiku ya halarci taron jam’iyya mai mulki ta ƙasar Ingila (HOTUNA)

Atiku tare da Firai Ministan Birtaniya

Sa’annan Atiku Abubakar ya samu rakiyar dan majalisar dattawa daga jam’iyyar PDP Ben Murray Bruce, wanda tare da shi suka halarci wannan muhimmin taro.

Shirye shiryen 2019? Atiku ya halarci taron jam’iyya mai mulki ta ƙasar Ingila (HOTUNA)

Atiku da Ben Bruce da dan majalisar Birtaniya Laim

Idan ba’a manta ba dai, Atiku ya dade yana da muradin shugabantar kasar nan, inda ya kwashe sama da shekaru 12 yana tsayawa takara a jam’iyyu daban daban.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ina Buhari yake?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel