Osinbajo ya kai ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Kano, Ganduje da iyalan Maitama Sule

Osinbajo ya kai ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Kano, Ganduje da iyalan Maitama Sule

- Mukaddashin Shugaban kasa ya jajanta ma iyalan Maitama Sule

- Osinbajo yayi hakan ne ta wata ziyarar ta'aziyya daya kai jihar Kano

A ranar Alhamis 6 ga watan Yuli ne mtaimakin shugaban kasa kuma mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyara jihar Kano don jajanta ma iyalan marigayi Miatama Sule Dan Masanin Kano.

KU KARANTA: Noma tushen arziƙi: An samu wasu dankalin turawa masu girman Doya a Kaduna (HOTUNA)

Osinbajo ya gana da mata, yaya, yan’uwa da abokan arzikin Maitama, inda yayi musu ta’aziyya tare da addu’an fatan Allah yayi masa rahama, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Osinbajo ya kai ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Kano, Ganduje da iyalan Maitama Sule

Osinbajo tare da iyalan Maitama Sule

Osinbajo ya bayyana ma iyalan mamacin cewar tun yana dan shekara 15 a jihar Legas ya fara haduwa da mariyagi Maitama, inda yace tun daga wannan lokacin ya zamto masa wani jigo abin koyi.

Osinbajo ya kai ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Kano, Ganduje da iyalan Maitama Sule

Iyalan Maitama Sule nayi masa maraba

Daga gidan mamacin sai Osinbajo ya garzaya fadar mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II, inda nan ma ya jajanta masa.

Osinbajo ya kai ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Kano, Ganduje da iyalan Maitama Sule

Sarkin Kano, Ganduje da osinbajo

Ga gaske yan Najeriy sun gaji da mulkin Buhari ne?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel