2019: Tsakanin El-Rufai da Shehu Sani, wa zai kada wani?

2019: Tsakanin El-Rufai da Shehu Sani, wa zai kada wani?

-Mahimancin zaman lafiya yafi karfin abar shi a hannun yan siyasa kawai

-Rashin jituwar yan siyasa ka iya raba kan jama’a da haifar da fitina

A ranar asabar 1 ga watan Yulin 2017, gidan rediyon Nagarta da ke garin Kaduna ya watsa wata hira da Senata Shehu Sani yayi da wasu manema labarai. Daga kalamun da ke fita bakin Senata Sani, kowa zai iya fahimta cewa dangantakan da ke tsakanin Senatan da gwamna Nasiru El-Rufai tana kara tabarbarewa ne.

Idan irin wannan rashin jituwan na faruwa a tsakanin yan siyasa musamman wanda je jami’iya daya, muna tsamanin manyan yan siyasa da wasu iyayen kasa da su kira su domin sulhunta su, domin kaman yadda masu iya magana kan fada “idan giwaye biyu na fada, kasa ke shan wahala”.

2019: Tsakanin El-Rufai da Shehu Sani, wa zai kada wani?

2019: Tsakanin El-Rufai da Shehu Sani, wa zai kada wani?

Alhakin kawo sulhu a tsakanin su baya rataya kadai bane a kan yan siyasa domin rashin jituwan nasu zai iya haifar da fituntunu da yawa da zai shafi jama’a baki daya.

Idan zamu iya tunawa da rikicin da ya faru a tsohuwar jami’iyar Peoples redemption Party (PRP) a Kano, lamarin ya tada hankalin kowa har da wanda babu ruwan su da siyasa a wannan lokacin. Ballewar Alhaji Abubakar Rimi daga jami’iayar PRP domin komawa jami’iyar National People’s Party (NPN) bai sa ya samu nasara a zaben gwamna a wannan lokacin ba.

KUMA KU KARANTA: Kiranye: Idan Senata Melaye bai gamsu da aikin mu ba, ya tafi kotu - INEC

Har ila yau, kadan ya rage da rikici ya balle a garin Kaduna a lokacin da majalisan jihar wanda mafiyansu yan jami’iyar NPN ne suka tsige gwamna Balarabe Musa na jami’iyar PRP duk da yana da magoya baya sasai wanda mafi yawancin su talakawa ne.

Abun lura anan shine siyasa abu ne wanda ya shafi kowane mutum, kuma rashin yin ta da tsafta zai iya kawo mana tashin hankali a tsakanin mu. Irin wannan rikicin jami’iyar shine ya watsu zuwa jihar Kogi da kano.

Gwamna El Rufai da sani dukansu mutane ne masu ilimi, hangen nesa da kuma kokarin inganta rayuwar talakan Najeriya. Hadin kan su domin yi ma jihar aiki zai yi tasiri sosai. Akwai darusa da yawa da zamu koya wasu kasashen da ke demokradiya. Misali a kasar Amurka, Uwargida Hillary Clinton ta soki Shugaba Barrack Obama a lokacin da suke zaben fitar da gwani amma bayan yayi nasara ya zama shugaban kasa, ya bata mukamin sakatariyar kasa kuma daga bisani ya bata goyon baya sosai a lokacin da tayi takara da Shugaba Donald Trump din jami’iyar Republican duk da batayi nasara ba.

Abin lura anan shine ya kamata yan siyasa su hada kansu waje guda domin samar ma talaka walwala da jin dadi a rayursa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel