An kama wani tsohon dan sanda da ya yi wa ‘yar shekara 9 fyade

An kama wani tsohon dan sanda da ya yi wa ‘yar shekara 9 fyade

Rundunar ýan sanda sun yi ram da wani tsohon dan sanda, DSP Chistopher Archibong (mai ritaya) kan laifin yi ma wata yarinya mai shekaru 9 fyade a Calabar, babban birnin jihar Cross-Rivers.

Kwamishinan ýan sandan jihar, Mista Hafiz Inuwa ya tabbatar da hakan a wani zama da ya yi da manema labarai a hedikwatan rundunar ýan sandan jihar.

A cewar kwamishinan, Archibong mai shekaru 55 a duniya ya aikata mummunan laifin ne a ranar 31 ga watan Mayu na shekarar 2017.

Inuwa ya kara da cewa mai laifin ya rinjayi yarinyar ne ta hanyar yaudara, sannan ya shigar da ita gidan shi wanda baá gama ba, yayinda ya nemi ta taya shi samo itacen jirgi.

An kama wani tsohon dan sanda da ya yi wa ‘yar shekara 9 fyade

An kama wani tsohon dan sanda da ya yi wa ‘yar shekara 9 fyade

Yarinyar ta yi bakin kokarinta don ganin ta kubuta daga hannun shi amma ya yi barazanar yi mata asiri idan bata amince ba.

KU KARANTA KUMA: An dakatar da Shugaban hukumar NHIS, kan zargin aikata zambaAn dakatar da Shugaban hukumar NHIS, kan zargin aikata zamba

Kwamishinan ya ce bayan jamián tsaro sun yi ram da shi kan aikata laifin, ya furta aikata mugun aikin.

A yanzu haka n gurfanar das hi a gaban kotu sannan kuma yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike a kan alámarin.

Sai dai Archibong ya karyata hakan ga manema labarai inda ya bayyana cewa duk shiri ne abun.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel