Shehu Sani ya fice daga taron bude sabon ofishin EFCC a Kaduna dalilin halartar El-Rufai

Shehu Sani ya fice daga taron bude sabon ofishin EFCC a Kaduna dalilin halartar El-Rufai

- Sanata Shehu Sani ya fice daga wani taro da akayi na bude ofishin EFCC a Kaduna

- Hakan ya samo usuli ne saboda halartan taron da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi

- A cewa Shehu Sani shi ba zai iya zama a taron dake cike da masu guntun kashi a duwawunsu ba

Sanatan dake wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya fice daga wani taro da aka shirya taron domin bude ofishin EFCC a Kaduna wanda aka gudanar a jiya Alhamis, 7 ga watan Yuli.

Duk roko da akayi ga masa kan ya zauna karda ya tafi ya ci turo domin sanatan ya bayyana cewa ba zai iya zama a gurin taron ba alhalin yana ganin masu gudun kashi a tsuliya sun halarci taron, a cewarsa bai kamata suna halartan irin wannan taro ba.

Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa EFCC ce ta gayyaci Shehu Sani gurin taron bude ofishinta reshen Kaduna, sannan dan adawarsa gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya halarci taron.

Shehu Sani ya fice daga taron bude sabon ofishin EFCC a Kaduna dalilin halartar El-Rufai

Shehu Sani ya fice daga taron bude sabon ofishin EFCC a Kaduna dalilin halartar El-Rufai

A cewar Sanatan: “Ban ga ta inda hukumar 'yaki da cin hanci da rashawa za ta iya gudanar da wani bancike a Kaduna ba idan dai irin wadannan mutane ne za su halarci bude sabon ofishin nata a Kaduna.”

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Sakkwato tayi babban rashi – KARANTA

Cikin wadanda suka halarci taron sun hada da wakolin Sarkin Zazzau, Sanata Sule Usman Hunkuyi, tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero da dai sauransu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel