Zamu kafa hukumar tattara kudaden da aka kwato daga barayin gwamnati - Malami

Zamu kafa hukumar tattara kudaden da aka kwato daga barayin gwamnati - Malami

- Kungiyar SERAP, ta sanar da yin nasara a karar da ta shigar

- Ta nemi gwamnatin tarayya da ta bayyana sunayen barayin gwamnati da adadin kudaden da suka kwato

- Shugaban kungiyar ministan shariá Abubakar Malami ne ya sanar da haka

Kungiyarnan dake tabbatar da adalci a harkokin tattalin arzikin kasa wato SERAP, ta sanar da yin nasara a karar da ta shigar wanda ta bukaci gwamnatin tarayya da ta bayyana sunayen mutanen da aka kwato kudaden sata daga hannunsu da kuma adadin abun da gwamnatin ta kwato daga gare su.

A baya gwamnatin tarayyan Najeriya ta sanar da shirinta na kafa wata kwamiti na musamman da zata dunga harhada kudaden da aka kwato daga hannun barayin gwamnati.

Alkalin alkalai kuma ministan shariá na tarayya, Abubakar Malami ne ya sanar da wannan ci gaban bayan wata kotun tarayya dake zaune a jihar Lagas ta yanke hukunci a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli, cewa gwamnati ta yi gaggawar sanar da sunayen barayin gwamnatin da suka sace kudaden kasar.

Zamu kafa hukumar tattara kudaden da aka kwato daga barayin gwamnati - Malami

Zamu kafa hukumar tattara kudaden da aka kwato daga barayin gwamnati inji Abubakar Malami

Sannan kuma kotun, ta nemi gwamnatin tarayya da ta bayyana adadin kudin da aka harhada zuwa yanzu.

KU KARANTA KUMA: An dakatar da Shugaban hukumar NHIS, kan zargin aikata zambaAn dakatar da Shugaban hukumar NHIS, kan zargin aikata zamba

Mai shariá Hadiza Rabiu Shagari ce ta yanke hukuncin cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tayi gaggawan sanar da sunayen na barayin gwamnati da yawan kudin da aka kwato daga hannunsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel