Dan halak: Ɗan Najeriya ya nuna halin amana, attajiran Najeriya sun mai 19 na arziki

Dan halak: Ɗan Najeriya ya nuna halin amana, attajiran Najeriya sun mai 19 na arziki

- Matashin nan daya mayar da N60,000 asusun gwamnati ya samu tagomashi

- Wasu attajirai sun bashi kyautan wanke talauci

Wani tsohon ma’aikaci dake cin gajiyar shirin tallafi na N-Power Joshua Daniel ya mayar da albashin watanni biyu da aka biyashi bayan ya fita daga tsarin, kimanin naira N60,000.

Cikin ikon Allah sai gashi wannan yaron kirki ya gamu da sakkaya nan da nan ba tare da bata lokaci ba, kamar yadda mashawarcin shugaban kasa akan hanyar samar da ayyuka ga matasa, Mista Afolabi Imoukhuede ya bayyana.

KU KARANTA: Allah wadai: Ya hallaka matarsa, bayan ya danƙara ma ýar aikinta ciki

Mista Afolabi yace wasu yan Najeriya masu hannu da shuni su 5 sun kira shuwagabannin N-Power inda suka bukaci a basu lambar asusun bankinsa, sa’anan kowannensu ya aika masa da N60,000, jimilla N300,000 kenan.

Dan halak: Ɗan Najeriya ya nuna halin amana, attajiran Najeriya sun mai 19 na arziki

Joshua

“Zuwa ranar Laraba, yan Najeriya mutum 5 sun sanya masa N300,000 a asusun bankinsa sakamakon halin rikon amana daya nuna.” Inji Afolabi.

Daga karshe ya shawarci sauran masu cin gajiyar shirin N-Power da suka samu wani aikin da suyi koyi da Joshua, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin Najeriya ce giwar AFirka?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Taran aradu da ka: wata Hajiya ta dauki gabaran biya ma Mijinta sadaki don ya yo mata kishiya

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel