Dandalin Kannywood: Hadiza Gabon ta ba masu yi mata tsegumin aure ansa

Dandalin Kannywood: Hadiza Gabon ta ba masu yi mata tsegumin aure ansa

- Hadiza Gabon ta yi bayani game da auren ta

- Hadiza Gabon ta ce shi aure lokaci ne

- Jarumar tace ita kanta yazu neman mijin take yi ido rufe

Fitacciyar jarumar Kannywood kuma kyakkyawa a fuska da jiki mai suna Hadiza Gabon ta yi karin haske game da masu yi mata nasiha da shagube akan wai taki tayi aure.

Jarumar bayan da maganganun suka je kunnen ta sai ta kada baki tace: "Shi aure lokaci ne kuma nufi ne na Allah, amma babu wata mace da zata yi fatan kaiwa kamar ni ba tare da tayi aure ba, kuma hankalin ta ya kwanta"

Dandalin Kannywood: Hadiza Gabon ta ba masu yi mata tsegumin aure ansa

Dandalin Kannywood: Hadiza Gabon ta ba masu yi mata tsegumin aure ansa

NAIJ.com ta samu labarin cewa Hadiza Gabon din ta kuma ci gaba da cewa: "Saboda haka nima ina fata kuma ina adduar Allah ya kawo min miji nagari na samu nima in zama amarya."

Indai ba'a manta ba a kwanan baya ne tsohuwar fitacciyar jarumar ta Kannywood watau Safiya Musa ta fito tana mai bada shawarar cewa ya kamata yan matan fim din suyi aure.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel