Allah wadai: Ya hallaka matarsa, bayan ya danƙara ma ýar aikinta ciki

Allah wadai: Ya hallaka matarsa, bayan ya danƙara ma ýar aikinta ciki

- Wani mutum ya kashe matarsa kuma yayi ma yar aikinsa ciki

- wannan lamari ya faru ne a jihar Filato

Kaico! Wannan abu da mai yayi kama? Jami’an Yansandan jihar Filato sun tabbatar da kama wani magidanci mai shekaru 40 mai suna Victor Dashit bayan ya hallaka matarsa ta hanyar shake mata wuya.

Shi dai wannan magidanci ya hallaka matar tasa ne a gonarsa dake kauyen Kangang a ranar 2 ga watan Yuli, inda bayan aikata aika aikan ne sai ya gayyaci dan uwansa don ya agaza masa su kai ta asibiti, inda yayi musu karyar cewar yanke jiki tayi ta fadi.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Sakkwato tayi babban rashi – KARANTA

Wani na kusa da iyalin, ya bayyana ma jaridar Daily Trust cewar ma’auratan na yawan samun rikici a tsakaninsu, amma rikicin yayi kamari ne tun bayan da matar ta kama mijin nata tirmi da tabarya da yar aikinsu akan gadonta.

Allah wadai: Ya hallaka matarsa, bayan ya danƙara ma ýar aikinta ciki

Kama mutum

Wannan yasa matar sallamar yar aikin, sai dai bayan watanni biyu yarinyar ta dawo ta bayyana musu cewa ta samu juna biyu, daga nan ne sai alaka ta karasa lalacewa tsakanin ma’auratan, hart a kai ga matar ta gudu daga gidan.

Majiyar NAIJ.com ta bayyana cewa jim kadan bayan Uwargida Irene ta dawo gidan mijinta ne sai ta samuy ciki tare da shi, sai dai kash! Rikicin ma’auratan bai tsaya ba, haka ne wata rana mijin ya shiga dukanta, har da shake mata wuya, sanadiyyar haka ta mutu, dan da take dauke dashi ma haka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda yansandan kashe yaron wata mata, Kalla:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel