Sharhi: Tasirin rashin lafiyar Buhari kan harkar tsaro da siyasar kasar nan

Sharhi: Tasirin rashin lafiyar Buhari kan harkar tsaro da siyasar kasar nan

- Ana zafaffan kalamai tsakanin kabilun kasar nan

- Rashin laiyar shugaba Buhari ta bada sabon fagen rawar dari

- Shafukan sada zumunta na zamani na kara tunzura lamarin

Anya kuwa ba rashin laiyar shugaba Buhari ce ke bada damar zaafar harkokin siyasa da tsaro a kasar nan ba?

A yawancin lokuta, kasashe masu wuyar taiyarwa, suna bukatar shugaba wanda ke iya bada tsoro, mai karfin fada aji, mai iya zaune tsiraru masu iya cefa sauran jama'a cikin shakku, ko yada tsanar juna.

Sharhi: Tasirin rashin lafiyar Buhari kan harkar tsaro da siyasar kasar nan

Sharhi: Tasirin rashin lafiyar Buhari kan harkar tsaro da siyasar kasar nan

A 'yan watannin nan, shafukan sada zumunta na zamani, da ma sauran kafafen yada labarai, na yada amon kin jinin juna, tsana, kabilanci, bambadanci, da ma addinanci, wanda ke nuna kamar akwai alamun rikici na iya ballewa a kowanne lokaci.

KU KARANTA KUMA: Ta'addancin Boko Haram a jihar Difa

Masana na ganin wannan na da alaka da rashin shugaba mai karfi a kasa, da ma yiwuwar tasa na iya karewa, kuma rashin tabbas na wa zai karbi ragamar shugabanci a nan gaba.

A makon jiya, kakakin majalisar wakilai na kasa, Yakubu Dogara, ya koka kan yadda za'a iya cewa, tsaron kasa ya gagari jami'an tsaro, inda a yanzu haka sojoji ke rike da harkar tsaro a jihohi 28 daga cikin jihohi 36 na kasar nan.

Makomar kasar Najeriya bata dogara kan mutum daya ba, amma kuma zababben shugaban kasa na taka muhimmiyar rawa a tsari irin na Dimokuradiyya, kuma musamman kasashe na Afirka masu yawan kabilu da banbancin addinai, kari da karancin ilimi.

A yanzu dai ana iya cewa idan ba shugaba Buhari ne ya warke ya dawo ba, akwai abubuwa marasa riba da yawa da ka iya shafar zamantakewa a Najeriya, a kudu da arewacin kasar, musamman a siyasar 2019.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel