Buhariyya: Tsarin tattalin arziki na Shugaba Buhari ya sami shiga kamus na Turanci

Buhariyya: Tsarin tattalin arziki na Shugaba Buhari ya sami shiga kamus na Turanci

- Kamus na Turanci ya shigar da sabuwar kalmar Buhariyya

- Buhariyya na nufin Buharism

- An sami kalmar daga halayen shugaba Buhari

Wikipedia, shafi na kamus na Turanci, mai kama da kundin kalmomi da sunaye na duniya, wanda ya fi kowanne shafi tara mutane a yanar gizo, ya shigar da kalmar Buhariyya cikin jaddawalin sunayenya, Buharism da Turanci, inda ya kira kalmar da irin tsarin tattalin arziki na Buhari musamman irin na wancan mulkin nasa.

Tsarin tattalin arziki na Shugaba Buhari ya sami shiga kamus na Turanci

Tsarin tattalin arziki na Shugaba Buhari ya sami shiga kamus na Turanci

An samo kalmar ne daga sunan shugaban, wanda ake gani shi ya kirkiri irin wannan tsari na farko a duniya.

A shekarun 1980-1990 dai, mulkin Buhari ya zamo wani sabon tsari wanda ya tattare tattalin arziki ya hade shi a matattara guda, kame barayin gwamnati, tottoshe hanyoyin asara daga ayyukan kwangila.

KU KARANTA KUMA: Ta'addancin Boko Haram ya leka DIfa

Duk da irin wannan kyakkyawan niyya ta irin wannan tsari na Buhariyya dai, hakan kuma na jawo takurewar tattalin arziki da ma tsaiko a harkokin kudi na gwamnati, musamman a lokuta irin wannan da sabon mulkin jam'iyyar APC ya kawo.

Buharism dai, wato Buhariyya a wurin Bahaushe, ana yawan alakanta ta da kuncin rayuwa, da talauci da ma rashin bin hanyoyin zamani na tafiyar da kudi.

A yadda kamus din ya nuna ma, ana ganin Buharism kamar wani sabon tsari na gurguzu mai dan saukaka wa talakka, kamar dai irin na tsohon shugaban Libya, marigayi Mu'ammar Gaddafi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel