Kotu a Zariya ta dakatar da El-Rufai daga rusa masarautun jihar

Kotu a Zariya ta dakatar da El-Rufai daga rusa masarautun jihar

- Wata kotun Kaduna ta ja kunnen gwamnatin jihar kan yunkurin rusa masarautar jihar da take yi

- Alkalin kotun ya ce gwamnatin ta dakatar da shirin nata har a kammala sauraron karar da aka shigar

- Wannan shine karo na biyu da kotun jihar ke dakatar da gwamnatin kan ci gaba da aiwatar da wannan kudiri nata

- Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da rusa masarautu sama da guda 4000 da aka kafa a jihar a shekarar 2001

Wata kotu dake a garin Zaria, jihar Kaduna ta ja kunnen gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Mallam Nasir El-Rufai kan cewa karda ta kuskura ta ci gaba da yunkurin ta na rusa masarautar jihar da ta sanar.

Alkalin kotun maishari’a BF Zubairu ya ce ya zama lallai gwamnatin ta dakatar da wannan shiri da takeyi har sai an kammala sauraron karar da aka shigar a kotun kan haka.

Wannan shine karo na biyu da kotun jihar ke dakatar da gwamnatin kan ci gaba da aiwatar da wannan kudiri nata.

Kotu a Zariya ta dakatar da El-Rufai daga rusa masarautun jihar

Kotu a Zariya ta dakatar da El-Rufai daga rusa masarautun jihar

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da rusa masarautu sama da guda 4000 da aka kafa a jihar a shekarar 2001.

KU KARANTA KUMA: An dakatar da Shugaban hukumar NHIS, kan zargin aikata zamba

Hakimai uku ne suka gabatar da karan a gaban kotu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel